'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Zamfara, an Tafka Barna mai Girma

'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Zamfara, an Tafka Barna mai Girma

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane sama da 20 bayan sun kai harin a cikin tsakar dare
  • Tsagerun ƴan bindigan sun kuma hallaka wasu mutane da suka ƙi yarda su tafi da su zuwa cikin daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane aƙalla 20 a wani hari da suka kai a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a garin Kaura-Namoda, hedikwatar ƙaramar hukumar Kaura-Namoda ta jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kuma kashe mata huɗu da suka ƙi yarda su bi su zuwa cikin daji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Zamfara

Ƴan bindigan sun afka garin ne da misalin ƙarfe 2:00 na daren ranar Asabar, inda suka riƙa harbe-harbe ba kakkautawa yayin da suke shiga gidaje suna sace mutane.

Wannan hari ya auku ne kwanaki kaɗan bayan ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Kaura-Namoda/Birnin Magaji a majalisar wakilai, Aminu Sani Jaji, ya bayyana cewa ƴan bindiga sun mamaye yankinsa.

Wani mazaunin garin da ya tsira daga sacewa, Abdullahi Mohammed, ya bayyana cewa ƴan bindigan sun shigo da babura kuma dukkaninsu na ɗauke da muggan makamai.

A cewarsa, sun riƙa shiga gida-gida inda suka fitar da mutum 24 domin sace su.

Ya ƙara da cewa mata huɗu aka kashe saboda sun ƙi bin ƴan bindigar zuwa daji.

Abdullahi Mohammed ya koka da cewa ƴan bindigan sun yi fiye da awa uku suna cin karensu ba babbaka a garin ba tare da jami’an tsaro sun kawo ɗauki ba.

"Ƴan bindigan sun zo da muggan makamai sun shigo garinmu da sassafe ranar Asabar lokacin da yawancinmu ke cikin barci. Sun fara harbi don razana mutane, shi ya sa muka tashi daga barci.

“Mun yi ƙoƙarin fuskantar su, amma da yawa daga cikinmu, har da ni kaina, muka gudu muka shiga daji domin gudun a kashe mu ko a sace mu."
"Bayan haka, suka fara shiga gidaje suna sace mutane, adadinsu 24 mafi yawansu mata da yara da ba su iya gudu ba."
“Sai dai sun kashe mata huɗu da suka ƙi bin su zuwa daji. Abin da ke faruwa a wannan yanki abin tsoro ne matuƙa, domin ƴan bindigan suna aiki yadda suka ga dama ba tare da matsin lamba daga jami’an tsaro ba."

- Abdullahi Mohammed

Jihar Zamfara
'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin ƴan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar don samun ƙarin bayani kan lamarin.

Sai dai, kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa ba shi a cikin Gusau a halin da ake ciki yanzu."

"Gaskiya yanzu bana cikin garin Gusau, amma zan bincika sai na ba ka bayani."

- DSP Yazid Abubakar

Sai dai, ba a sake jin ta bakin kakakin ƴan sandan ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan bindiga sun ba karnuka jarirai

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsagerun ƴan bindiga sun ba karnuka wasu jarirai da suka yi garkuwa da iyayensu a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun ba da jariran ne ga karnukan bayan an haifesu lokacin da iyayensu ke tsare a hannunsu sakamakon garkuwa da su da aka yi.

Mummunan lamarin ya ƙara nuna irin matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng