Kuma dai: 'Yan Bindiga Sun Sake kai Harin Ta'addanci a Plateau, An Yi Barna

Kuma dai: 'Yan Bindiga Sun Sake kai Harin Ta'addanci a Plateau, An Yi Barna

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'asa a wani sabon harin ta'addanci da suka kai a cikin jihar Plateau
  • Miyagun sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi bayan sun farmaki mutanen ƙauyen Wereng Camp a ƙaramar hukumar Riyom
  • Sabon harin da ƴan bindigan suka kai ya jawo an samu asarar rayukan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba tare da jikkata wasu daban

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Ƴan bindiga sun hallaka aƙalla mutane takwas a wani sabon hari da suka kai a ƙauyen Wereng Camp da ke cikin ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Plateau.

Ƴan bindigan waɗanda suke ɗauke da makamai sun kai harin ne kan mutanen ƙauyen a cikin dare.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
'Yan bindiga sun kashe mutum 8 a Plateau Hotp: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Ƴan bindiga sun kai sabon hari a Plateau

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kuma ƙona gidaje da dama, tare da kwashe kayan abinci daga cikin gidajen da suka lalata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun dira garin cikin daren ranar Laraba inda suka riƙa harbe-harbe ba kakkautawa akan mazauna yankin.

Wasu mutane da dama sun jikkata, kuma a halin yanzu suna samun kulawa ta musamman a asibiti.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa yara da tsofaffi ne harin na ƴan bindigan ya fi ritsawa da su.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Ƙoƙarin samun tabbaci daga hukumomin tsaro kafin a fitar da wannan rahoto ya ci tura.

Legit Hausa ta kira layin wayar kakakin ƴan sandan jihar Plateau domin jin ta bakinsa, sai dai wayar ta sa ba ta shiga ba.

A baya-bayan nan, ƙauyuka da dama a ƙananan hukumomin Mangu, Barkin Ladi, Bokkos da Riyom sun sha fama da hare-haren ƴan bindiga, lamarin da ke kara tayar da hankalin jama’a a faɗin jihar.

'Yan bindiga sun kai sabon hari a Plateau
'Yan bindiga sun yi kashe-kashe a Plateau Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Saboda tsananin damuwa kan wannan mummunan lamarin, gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya roƙi gwamnatin tarayya da ta shiga cikin lamarin domin kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa al’umma.

Gwamna Mutfwang ya kuma ayyana dokar hana amfani da babura daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a faɗin jihar, har sai zuwa wani lokaci da za a sanar.

Hakazalika, gwamnan ya kuma haramta kiwon dabbobi da daddare a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na ɗaya daga cikin hanyoyin da gwamnati ke ɗauka domin dawo da zaman lafiya da kuma ƙarfafa tsaro a jihar.

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun hallaka mutane shida a wani hari da suka kai a jihar Plateau.

Ƴan bindigan sun hallaka mutanen ne a ƙauyukan Marit da Ghashish da ke ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta jihar.

Harin da miyagun ƴan bindigan suka kai kuma, ya jawo sanadiyyar jikkata wasu mutanen daban waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng