An Yi Gumurzu Mai Tsanani da Ƴan Bindiga Suka Kai Farmaki Mahaifar Gwamna a Najeriya
- Yan bindiga sun kai farmaki kan shingen bincike a mahaifar gwamnan Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo ranar Alhamis
- Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa an yi gumurzu da maharan kuma jami'an tsaro sun samu nasarar kashe biyu daga cikinsu
- Jami'in hulɗa da jama'a na ƴan sandan Anambra, SP Tochukwu Ikenga ya ce tuni aka tura ƙarin dakaru domin farauto sauran maharan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan shingen binciken ababen hawa na jami'an tsaro da ke Isuofia, garin su Gwamna Charles Chukwuma Soludo.
Ƴan bindigar sun kai mummunan hari mahaifar mai girma gwamnan da ke karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra a daren ranar Alhamis.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa a yayin harin, an kashe wasu daga cikin ’yan bindigar guda biyu, yayin da wani jami’in ’yan sanda ya samu munanan raunuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an tsaro sun fafata da ƴan bindiga
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Anambra ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana takaicinta kan ƙaruwar hare-haren ƴan ta'adda.
Kwamishinan ’yan sandan Anambra, Ikioye Orutugu, ya bayyana harin a matsayin kalubale ga hadin gwiwar da aka samu tsakanin al’umma da jami’an tsaro da nufin kawar da miyagu daga jihar.
A cikin wata sanarwa da ta fito daga rundunar ’yan sandan jihar, ta ce jami’an tsaro na hadin gwiwa sun fatattaki maharan bayan artabu mai zafi.
An kashe ƴan bindiga 2 a Anambra
Sanarwar ta tabbatar da cewa dakarun ƴan sanda sun yi nasarar hallaka biyu daga cikin ƴan bindigar a musayar wuta.
"A lokacin gumurzu, an kashe biyu daga cikin maharan. Amma abin takaici, daya daga cikin jami’an tsaronmu ya samu raunuka, sannan maharan sun kona motar aiki ta jami’an tsaro,” inji sanarwar.
Rundunar ta kuma ce maharan sun tsere bayan sun bar wata motar Toyota Sienna a wurin da harin ya auku.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da cewa zuwa yanzu zaman lafiya da ya dawo a yankin.

Asali: UGC
An tura jami'an tsaro zuwa dazuka
Haka nan kuma, kakakin ƴan sanda ya ce an tura karin jami’an tsaro cikin shirin ko ta kwana zuwa garin domin ci gaba da bincike da farautar wadanda suka tsere cikin dazuka.
CP Orutugu ya tabbatar da cewa rundunar ƴan sanda za ta ci gaba da kokarin cafke wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
Ya kuma jaddada kudurin rundunar ƴan sanda na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar Anambra, Premium Times ta rahoto.
An kama wanda ya kashe ɗan Majalisa
A wani labarin, mun kawo maku cewa ƴan sanda sun yi nasarar sake kama wanda ake zargi da hannu a kisan ɗan Majalisar Dokokin Anambra, Justice Azuka.
Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin ya tsere bayan kama shi a kwanakin baya, amma yanzu ƴan sanda sun sake yin ram da shi a Asaba.
Kwamishinan ‘yan sandan Anambra ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda aka bari wanda ake zargin ya tsere a baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng