Sabon Rikici: Trump Ya Dauki Wani Matakin Rusa Iran, Tehran Ta Nuna Jan Wuya
- Amurka ta ƙaddamar da wani sabon shirin matsin tattalin arziki kan Iran, tare da shirin katse hanyoyin samun kuɗin gwamnatin Tehran
- Ministan Baitul Malin Amurka, Scott Bessent, ya ce za su yi amfani da takunkumi wajen hana ƙasashe da kamfanoni ci gaba da hulɗa da Iran
- Iran ta yi watsi da sabon shirin na Amurka, yayin da ministan harkokin wajenta, Abbas Araghchi, ya ce takunkumin tattalin arziki ba sabon abu ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Gwamnatin Amurka ta ƙaddamar da wani sabon shirin matsin tattalin arziki kan Iran mai suna “Operation Economic Outcast”, da nufin katse hanyoyin samun kuɗin gwamnatin Tehran.
Ministan Baitul Malin Amurka, Scott Bessent, ya bayyana cewa sabon shirin zai shafi dukkan manyan hanyoyin samun kuɗin Iran, ciki har da fannin man fetur.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki zafi, ya sake fallasa abin da yan Najeriya ba su sani ba kan tallafin man fetur

Source: Facebook
Al Jazeera ta rahoto cewa Amurka za ta yi ƙoƙarin hana ƙasashe da kamfanoni a faɗin duniya ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci da Iran.
Matakin da Amurka ta dauka
Scott Bessent ya ce manufar gwamnatin Amurka ita ce katse duk wata hanyar tattalin arziki da ke taimakawa gwamnatin Iran ta ci gaba da samun kuɗin shiga.
Ya bayyana cewa ƙasashe da kamfanonin da ke taimakawa wajen sayar da man Iran ko sauƙaƙa hanyoyin samun kuɗin za su iya fuskantar takunkumin Amurka.
Fadar White House ta wallafa cewa Bessent ya ce:
“Manufarmu ita ce katse duk wata hanyar tattalin arziki da ke ci gaba da tallafa wa wannan gwamnati har sai Tehran ta tsinci kanta ita kadai.”
Ya kuma ce ƙasashe a duniya za su fuskanci zaɓi tsakanin ci gaba da hulɗa da Amurka ko kuma Iran, saboda haɗarin takunkumin na biyu da Washington ke shirin amfani da shi.
Takunkumin Amurka ga Iran
Amurka ta bayyana cewa sababbin takunkumin za su mayar da hankali kan manyan hanyoyi guda biyar da Iran ke amfani da su wajen ci gaba da samun kuɗi.
Hanyoyin sun haɗa da kadarorin da suke intanet, fasaha, zinare, harkokin jiragen sama da kuma jigilar kayayyaki ta ruwa.
Amurka ya kuma sanar da kakaba sabon takunkumi kan kamfanoni, jiragen ruwa da wasu mutane 60 da ke ƙasashe daban-daban, ciki har da Hadaddiyar Daular Larabawa, China, Singapore da Switzerland.
A nasa bangaren, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce sabbin takunkumin ba wani sabon abu ba ne ga ƙasar.

Source: Getty Images
Ya ce Amurka ta dade tana amfani da irin wannan tsari wajen matsa wa Iran lamba, amma Tehran ba za ta yi kasa a gwiwa ba saboda matsin tattalin arziki.
Batun tsige Trump a Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yana fargabar za a sake yunƙurin tsige shi daga mulki idan jam'iyyar Democrat ta samu rinjaye a majalisa.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ware malaman musulunci yana biyansu duk wata, ya fada masu irin wa'azin da za su yi
Trump ya yi wannan furuci ne yayin wani gangamin siyasa a Myrtle Beach da ke jihar South Carolina, inda ya roƙi magoya bayansa su fito ƙwansu da kwarkwatarsu domin zaɓen.
Ya ce idan jam'iyyar Republican ta rasa rinjaye, Democrat za su iya ƙoƙarin tsige shi tare da sauya wasu daga cikin manufofin da gwamnatinsa ta aiwatar.
Asali: Legit.ng
