Tirkashi: An Gwabza tsakanin Sowore da Amaechi a Wurin Taro

Tirkashi: An Gwabza tsakanin Sowore da Amaechi a Wurin Taro

  • Chibuike Amaechi da Omoyele Sowore sun yi musayar kalamai masu zafi a taron kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da aka gudanar a Fatakwal, jihar Rivers
  • Sowore ya soki tsohon gwamnan jihar Rivers kan ayyukan da ya aiwatar a lokacin mulkinsa da kuma lokacin da yake ministan sufuri
  • Amaechi ya kare tarihin mulkinsa, inda ya kalubalanci Sowore da ya nuna irin kwarewarsa a harkar mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Chibuike Amaechi, tsohon gwamnan jihar Rivers kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na African Democratic Congress (ADC), ya yi musayar kalamai da Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na Action Congress (AAC).

Amaechi da Sowore sun gwabza ne a taron kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da aka gudanar a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers, ranar Litinin, 24 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Amaechi: Mataimakin Atiku ya bukaci 'yan Najeriya kada su zabi ADC, an ji dalili

Sowore ya yi musayar yawu da Amaechi
Omoyele Sowore da tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi Hoto: @yelesowore, @chibuikeamaechi
Source: Twitter

The Cable ta ce Amaechi ya mayar da martani ne ga sukar da Sowore ya yi cewa wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya, ciki har da tsohon ministan sufuri, sun taka rawa wajen jefa kasar cikin matsalolin tattalin arziki.

Sowore ya soki Amaechi da sauran ‘yan Siyasa

Yayin da yake jawabi ga mahalarta taron, Sowore ya soki ‘yan siyasar da suka dade suna kan madafun iko, inda ya bukaci masu kada kuri’a su yi watsi da alkawuran da wasu ‘yan siyasa ke maimaitawa duk da cewa sun taba rike mukamai a gwamnati.

“Don Allah, don Allah, kada ku bari wadannan ‘yan siyasa su yaudare ku,” Sowore ya gargadi mahalarta taron.

Da yake magana kan wata magana da ya ce Amaechi ya taba yi a baya, Sowore ya ce:

“Abu daya da Amaechi ya fada kuma ya birgeni. Ya ce ban da Sowore da Abiola, sauranmu da muka taba kasancewa a gwamnati mun gaza. Ba su da wani dalilin dawowa.”

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Sowore ya koma kan lokacin da Amaechi ya kasance gwamnan jihar Rivers da kuma ministan sufuri, inda ya soki yadda aka tafiyar da wasu manyan ayyukan jihar da kuma yadda aka kashe kudaden gwamnati.

Sowore ya tuna batun jirgin kasa

Sowore ya ce:

“Idan ana magana kan tallafin gwamnati, manufofin sufuri suna da muhimmanci. Muna da tsohon gwamnan jihar Rivers a nan, Amaechi, wanda ya gina layin dogo da bai kai ko ina ba. Da wannan layin dogo yana aiki, da tallafin gwamnati yana amfanar mutanen Rivers.”
“Kuma ba za mu iya yin biris da cewa wadanda suka taba mulki a baya sun ki tallafa wa mutanensu ba.”

Sowore ya kuma tabo batun rikicin ma’aikata a lokacin da Amaechi yake gwamnan jihar Rivers.

“Ba ka tallafa wa ilimi a jiharka ba. Malamai da likitoci sun shiga yajin aiki na tsawon watanni 13! Za ku iya son sa a matsayin mutum, amma bai yi abin da ya kamata a matsayin gwamna ba. Wannan ita ce gaskiya,” in ji shi.

Amaechi ya kare mulkinsa

Sai dai tsohon gwamnan jihar Rivers ya kare tarihin mulkinsa, inda ya kalubalanci Sowore da ya nuna irin kwarewar da yake da ita wajen gudanar da gwamnati.

Kara karanta wannan

Masana'antar fim ta yi rashi, fitaccen jarumi a Najeriya ya bar duniya

Amaechi ya kawo wasu manyan ayyukan layin dogo da aka gudanar a lokacin da yake ministan sufuri, ciki har da layin dogo na Lagos zuwa Ibadan da kuma Abuja zuwa Kaduna.

“Su waye suka fito daga Legas? Layin dogo na Legas zuwa Ibadan yana aiki ko ba ya aiki? A lokacin da nake mulki, yana aiki. Ban san abin da ke faruwa a karkashin Tinubu ba. Akwai layin dogo na Abuja zuwa Kaduna, yana aiki ko ba ya aiki?” Amaechi ya tambaya.

Sowore ya yi kokarin katse shi ta hanyar sake tabo tarihin Amaechi a matsayin gwamnan Rivers, amma tsohon ministan ya dakatar da shi.

Amaechi ya yi musayar yawu da Sowore
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Twitter

Amaechi ya nuna ayyukan Rivers

Amaechi ya kalubalanci Sowore da ya zagaya jihar domin duba ayyukan da ya ce ya aiwatar a lokacin da yake gwamnan jihar.

“Ina lauyoyin Rivers? Don Allah ku kai Sowore yawon gani da ido. Ina lauyoyin Rivers da suke nan? Ku kai Sowore yawon gani da ido." In ji shi.

Amaechi ya ci gaba da lissafa wasu ayyukan da ya ce ya aiwatar a jihar.

“Na ce ni ne na gina wannan hanya. Na gina wannan hanyar. Na gina wannan makarantar firamare. Na gina waccan makarantar firamare,” ya ce.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 6, malaman addini 500 sun bayyana dan takarar shugaban kasarsu a 2027

Daga nan sai ya juya wajen Sowore ya tambaye shi:

“Sowore, mene ne kwarewarka? Idan ‘yan siyasa suna magana, ku rufe bakinka." In ji shi.

Rawar da Amaechi ya taka a nasarar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce ya taka rawawajen nasarar marigayi Muhammadu Buhari.

Amaechi ya bayyana cewa shi ne, ba Shugaba Bola Tinubu ba, ya taka muhimmiyar rawa wajen sanya marigayi Muhammadu Buhari zama shugaban ƙasa a shekarar 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng