"Dalilin da Ya Sa Matsalar Rashin Tsaro Ta Ta'azzara a Mulkin Buhari'

"Dalilin da Ya Sa Matsalar Rashin Tsaro Ta Ta'azzara a Mulkin Buhari'

  • Tsohon jami'in DSS Dennis Amachree ya ce rashin kulawar gwamnati ga barazanar ta'addanci, 'yan bindiga da garkuwa da mutane ya taimaka wajen ƙara tabarbarewar tsaro a Najeriya
  • Ya kuma zargi manyan jami'an gwamnati da cin hanci da rashawa da kuma biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane
  • Amachree ya ce biyan kuɗin fansa ya taimaka wajen ɗaukar nauyin ta'addanci da garkuwa da mutane a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Dennis Amachree, ya bayyana dalilan da ya ce suka sa rashin tsaro ya yi kamari a Najeriya a lokacin mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Dennis Amachree ya bayyana dalilin ne a cikin sabon littafinsa mai suna DSS@ 40: My Journey behind the Shield.

An zargi Buhari da sakaci kan rashin tsaro
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce a cikin littafin, Amachree ya zargi gwamnatin da rashin mayar da hankali ga barazanar da ke ƙara ta'azzara ta'addanci, 'yan bindiga da garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

An gwabza fada tsakanin jami'an tsaro da ƴan bindiga a Katsina, an rasa rayuka

Ya kuma zargi manyan jami'an gwamnati da cin hanci da rashawa da kuma biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane, lamarin da ya ce a zahiri ya taimaka wajen ɗaukar nauyin ta'addanci da garkuwa da mutane a Najeriya.

Rashin tsaro ya ƙaru a zamanin Buhari

Marubucin ya ce lokacin mulkin Muhammadu Buhari ya kasance wani muhimmin lokaci da barazanar tsaro ta yaɗu sosai, yayin da rashin kulawar gwamnati ya zama a bayyane.

Duk da kasancewarsa tsohon janar na soja, Amachree ya ce ana kallon gwamnatin a matsayin wadda ta yi “kaɗan ko ta gaza katabus” wajen dakile barazanar ta'addanci, 'yan bindiga da garkuwa da mutane da ke ƙaruwa.

Ya ce rashin ingantaccen martani ya ƙara haifar da ra'ayin cewa shugabancin bai san yadda ake tafiyar da mulkin dimokuraɗiyya ba ko kuma bai damu da hakan ba.

Kalaman Buhari sun jawo suka

Amachree ya ce kalaman shugaban ƙasar, kamar kiran matasan Najeriya da “malalata” yayin wasu tafiye-tafiyensa na ƙasashen waje, an ɗauke su a matsayin ƙara wa rashin aikin yi da ya addabi jama'a muni.

Ya ce hakan ba kawai ya ɓata sunan Najeriya ba ne, har ma ya ƙara nisantar da ɗimbin jama'a da suka ji cewa gwamnati ta yi watsi da su.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Matawalle ya ba sojoji sabon umarni kan 'yan ta'adda

An zargi gwamnati da biyan kudin fansa

Baya ga yawan cin hanci da rashawa da ake zargin manyan jami'an gwamnati da aikatawa, Amachree ya tabo zargin cewa gwamnatoci sun yi ta biyan 'yan bindiga biliyoyin Naira a matsayin kuɗin fansa.

Amachree ya ce musanta zargin da jami'an gwamnati suka yi daga baya, wanda 'yan bindiga irin su Bello Turji suka fallasa, ya rusa amincewar jama'a da gwamnati.

Ya ce hakan ya kuma tabbatar da cewa gwamnati tana taimakawa wajen ɗaukar nauyin barazanar da take ikirarin cewa tana yaƙi da ita.

An zargi Buhari da sakaci kan rashin tsaro
Marigayi Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasar Najeriya Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Rikicin talakawa da masu mulki

Ya kuma bayyana 'yan siyasar zamanin mulkin a matsayin masu adawa da muradun jama'a, yana mai cewa tushen matsalar tsaro ba koyaushe yake tsakanin ƙabilu ba.

A cewarsa, sau da yawa rikicin yana tsakanin masu mulki da talakawan da ke aiki tukuru.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sanye da kayan sojoji sun yi ta'asa bayan kai wani hari a jihar Sokoto.

Hatsabiban 'yan bindiga sun kashe akalla mutane hudu a harin da suka kai a Unguwan Lalle da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng