"Ba Zai Yiwu ba"; Peter Obi Ya Tsage Gaskiya Ya Fadi Alkawarin da ba Zai Daukarwa 'Yan Najeriya ba
- Peter Obi wanda ke takarar shugaban kasa a zaben 2027 ya bayyana alkawarin da ba zai yi wa ’yan Najeriya ba idan aka zabe shi shugaban ƙasa
- Dan takarar NDC ya ce zai mayar da hankali wajen inganta samarwa da isar da wutar lantarki tare da rarraba ta a faɗin ƙasar
- Obi ya ce za a iya samar da fiye da megawatt 10,000, amma matsalar yanzu ita ce rashin isar da wutar da ake samarwa da kuma rarraba ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Peter Obi, dan takarar shugaban ƙasa na NDC a zaben 2027, bayyana alkawarin da ba zai iya daukarwa 'yan Najeriya ba.
Peter Obi ya ce ba zai yi wa ’yan Najeriya alkawarin samun wutar lantarki mai ɗorewa ta sa’o’i 24 cikin shekaru hudu ba idan aka zabe shi shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta hango kura kurai a kalaman Obi, ta yi masa zazzafan martani

Source: Facebook
Peter Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Channels Tv a daren ranar Lahadi, 27 ga watan Yulin 2026.
Wane alkawari ne Peter Obi ba zai yi ba?
Obi ya ce inganta wutar lantarki zai kasance cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta fi ba muhimmanci, amma ba zai yiwu a yi alkawarin samar da wutar sa’o’i 24 a faɗin ƙasar cikin shekaru hudu ba.
“Ba zan gaya musu cewa zan ba su ingantacciyar wutar lantarki mai ɗorewa ta sa’o’i 24 cikin shekaru hudu ba."
“Ba zai yiwu ba, domin idan kana son gina tashar samar da wutar lantarki, zai ɗauki kusan shekaru hudu kafin ka kammala gina ta."
“Idan kana son gina layukan isar da wutar lantarki da inganta su, hakan ma zai ɗauke shekaru da dama.” In ji shi
Obi ya yi alkawarin samar da Megawatt 10,000
Obi ya ce a maimakon yin alkawuran da ba za a iya cika su ba, gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen inganta samar da wutar lantarki, isar da ita da kuma rarraba ta domin samun ingantaccen wutar lantarki a faɗin ƙasar.
Ya yi alkawarin tabbatar da cewa Najeriya za ta iya samarwa, isarwa da rarraba aƙalla megawatt 10,000 na wutar lantarki a kai a kai.

Source: Facebook
Peter Obi ya ce babbar matsalar ƙasar a yanzu ta fi kasancewa wajen isar da wutar da ake samarwa da kuma rarraba ta, ba wai wajen samar da ita kawai ba.
“Za mu iya samar da fiye da megawatt 10,000. A yau ma muna yin hakan, muna samar da fiye da 10,000, amma ba za mu iya isar da wannan wutar ba."
“Na ce za mu iya samar da fiye da 10,000, mu isar da ita sannan mu rarraba ta.” In ji shi.
Peter Obi ya ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya soki salon isar da sakon Shugaba Bola Tinubu.
Peter Obi ya roƙi shugaban kasar da ya riƙa yi wa ’yan Najeriya magana kai tsaye game da halin da ƙasar ke ciki.
Asali: Legit.ng
