'Yan Bindiga kusan 200 Sanye da Kayan Sojoji Sun Yi Ta'asa a Jihar Sokoto

'Yan Bindiga kusan 200 Sanye da Kayan Sojoji Sun Yi Ta'asa a Jihar Sokoto

  • 'Yan bindiga da ake zargin sun sanya kayan sojoji sun kai hari Unguwan Lalle da ke karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto
  • Maharan da yawansu ya kai kusan 200 sun kwashe kusan sa'o'i shida suna wawushe kaya a gidaje da shaguna tare da sace dabbobi
  • 'Yan bindigar sun kai harin ne jim kadan bayan sojoji sun bar kauyen bayan sun mayar da martani kan wani hari da aka kai da rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Akalla mutane hudu ne aka kashe, yayin da wasu da dama suka samu raunuka bayan wasu 'yan bindiga da ake zargin sun sanya kayan sojoji sun kai hari Unguwan Lalle da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto

Harin wanda ya fara da misalin karfe 8:00 na dare ranar Lahadi ya ci gaba har zuwa karfe 2 na safiyar Litinin, inda maharan suka wawushe gidaje da shaguna tare da sace adadin dabbobin da ba a tantance ba.

Kara karanta wannan

An gwabza fada tsakanin jami'an tsaro da ƴan bindiga a Katsina, an rasa rayuka

'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ce mazauna yankin sun ce maharan sun shafe kusan sa'o'i shida suna gudanar da harin duk da cewa jami'an tsaro sun kasance a yankin tun da farko a wannan rana.

Yadda harin 'yan bindigan ya faru

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan dauke da manyan makamai, wadanda aka kiyasta yawansu ya kai kusan 200, sun shigo garin daga wurare daban-daban, inda da farko suka yaudari mazauna yankin cewa jami'an tsaro ne

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa:

"Wadanda muka gani sun sa mun yi zaton sojoji ne saboda suna sanye da kayan sojoji. Sun kewaye kauyen, suka bude wa duk wanda ke kokarin tserewa wuta, suka binciki gidajenmu, suka tafi da dabbobinmu tare da kwashe kayayyaki daga shagunanmu."

An bayyana sunayen wasu daga cikin wadanda aka kashe da cewa Bilyaminu Wakkala da Danbaki Tulunawa, yayin da sauran mutum biyun da suka mutu mazauna kauyen Kongurus ne da ke kusa

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace babban dan siyasa, matarsa da 'ya'yansa a Zamfara

A cewar mazauna yankin, mutanen biyun kan kwana a Unguwan Lalle saboda rashin tsaro da ya addabi garinsu, kafin su koma gida da rana.

Mazauna yankin sun ce harin ya faru ne kasa da awa guda bayan sojojin da suka mayar da martani kan wani harin 'yan bindiga daban sun bar kauyen.

Wani mazaunin yankin ya ce sojojin sun isa wurin ne da motocin yaki guda biyu bayan an zargi 'yan bindiga da kashe wani manomi da rana.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

An kasa samun martanin hukumomi a lokacin hada wannan rahoto, yayin da shugaban karamar hukumar Sabon Birni, Alhaji Ayuba Hashimu, da dan majalisar wakiltar mazabar Sabon Birni ta Arewa a majalisar dokokin jihar Sokoto, Hon. Aminu Boza, ba su amsa kiran wayar da aka yi masu ba.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa'i, ya tabbatar da kashe wani manomi a yankin, amma ya ce ba a yi masa bayani kan harin da aka ruwaito an kai wa al'ummar ba.

"Na samu rahoton da ya tabbatar da kashe mutum daya a yankin ranar Lahadi. Sai dai har yanzu ba a yi mini bayani kan wani harin da aka ruwaito an kai wa al'ummar ba," in ji shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake ta'addanci a Zamfara, an kashe manoma a gonakinsu

'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan bindiga sun sace babban alkali

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan bindiga dauke da manyan makamai sun yi garkuwa da Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza.

'Yan bindigan sun sace babban alkalin ne a gidansa da ke kan titin Zogirma a ƙaramar hukumar Bunza, jjim kaɗan bayan alƙalin ya dawo daga wata tafiya zuwa Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng