"Ka Fito": Peter Obi Ya ba Tinubu Shawara bayan Gano Kuskuren da Yake Yi

"Ka Fito": Peter Obi Ya ba Tinubu Shawara bayan Gano Kuskuren da Yake Yi

  • Peter Obi ya soki salon isar da sakon Shugaba Bola Tinubu, yana mai roƙon shugaban ya riƙa yi wa ’yan Najeriya magana kai tsaye
  • Dan takarar NDC ya ce za a fitar da Najeriya daga talauci ne ta hanyar samar da ababen amfani, musamman ta hanyar noma
  • Obi ya ce idan aka samar da tsaro a gonaki, tare da farfaɗo da masana’antu da samar da rancen kuɗi mai sauƙi, Najeriya za ta iya ƙirƙirar ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya soki salon isar da sakon Shugaba Bola Tinubu.

Peter Obi ya roƙi shugaban kasar da ya riƙa yi wa ’yan Najeriya magana kai tsaye game da halin da ƙasar ke ciki.

Peter Obi ya ba Tinubu shawara
Peter Obi na jawabi a wajen wani taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan halin da ƙasar ke ciki a wata hira ta musamman da shirin Sunday Politics na Channels Tv a ranar Lahadi, 26 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya gaji': Obi ya ce matsalolin Najeriya sun fi karfin shugaban kasa

Wace shawara Obi ya ba Tinubu?

Dan takarar shugaban kasar ya ce ’yan Najeriya na son jin magana kai tsaye daga Tinubu, wanda suka zaɓa ya jagorance su, maimakon hadimansa a gwamnati.

Ya zargi shugaban ƙasar da dogaro da mataimakansa da masu magana da yawunsa wajen bayyana manufofin gwamnatinsa ga ’yan Najeriya.

“Ba ma ‘audio hope’ ba ne, domin mutumin da muka zaɓa ma ba ya sake magana da mu."
“Mutumin da muka zaɓa a wannan ƙasa shi ne Bola Tinubu. Ba ya sake magana da mu; ya shiga Aso Rock ya mayar da shi kamar wata maboya. Muna son ya fito daga wannan maboya ya yi wa jama’a magana.” In ji shi

Obi ya soki salon Tinubu

Tsohon gwamnan ya tambayi salon da shugaban ke amfani da shi wajen magana kan muhimman batutuwan ƙasa, inda ya kawo batun ce-ce-ku-ce da ya taso kan hukumar PFIPC a matsayin misali.

Obi ya kuma yi alkawarin bai wa harkar noma muhimmanci, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen fitar da Najeriya daga ƙasar da ke dogaro da amfani da kayayyakin da ake samarwa a wasu wurare zuwa ƙasar da ke samar da nata kayayyaki.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bani, Shugaba Tinubu ya fadada rundunar sojojin Najeriya

Noma zai taimaki Najeriya

“Wannan ƙasa za ta iya samar da isasshen abin da za mu ci, kuma za mu iya samun kuɗi mai yawa daga noma fiye da abin da muke samu daga man fetur, domin a yau muna da faɗaɗɗun filayen noma da ba a noma su."
"Hanya ɗaya tilo ta fitar da Najeriya daga talauci, ko ma ta haɓaka GDP da gaske, ita ce samar da kayayyaki, ba amfani kawai ba. Wannan samarwa ta fara ne da noma, wanda zai ba ka abincin da kake buƙata, albarkatun da masana’antunka za su yi amfani da su, da ayyukan yi. Wannan nasara ce ga kowa.” In ji shi.
Peter Obi ya soki Shugaba Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na NDC a zaben 2027, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

A cewarsa, Najeriya na iya zama babbar ƙasar da ke fitar da kayan abinci zuwa ƙasashen waje, ciki har da shinkafa.

“Bangladesh a yau tana samar da kusan tan miliyan 15 zuwa 16 na shinkafar da ba a niƙa ba… yanzu tana cikin ƙasashe uku ko huɗu da suka fi kowace ƙasa samar da shinkafa a duniya,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Fashola: Tsohon gwamna ya fadi dalilin kin sukar gwamnatin Tinubu

Ya ce idan Bangladesh ta iya samun irin wannan nasara duk da ƙarancin filayen da take da su, to Najeriya da take da faɗaɗɗun filayen noma za ta iya yin abin da ya fi haka.

Peter Obi ya magantu kan zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya bayyana cewa ya na da yakinin zai yi nasara.

Peter Obi ya bayyana cewa zaɓen ba fafatawa ce ta siyasa tsakaninsa da gwamnati mai ci ba, illa dai tsakanin ‘yan Najeriya da gwamnatin ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng