Gwamna da Jam'iyya Sun Kyale dan Takararsu, Sun Goyi bayan Tazarcen Tinubu a 2027
- Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da shugabannin jam’iyyar Accord na ƙasa sun amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027
- Shugabannin jam’iyyar sun ce ya kamata gwamnatin Tinubu ta kammala manyan ayyukan tituna da ababen more rayuwa da ta fara
- Sun kuma yi gargaɗi kan tashin hankali, tsoratarwa da magudin zaɓe a zaɓen gwamnan Osun na watan Agustan shekarar 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Osogbo, Jihar Osun – Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, da shugabannin jam’iyyar Accord na ƙasa, sun nuna goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu.
Gwamna Adeleke da shugabannin na Accord sun amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

Source: Facebook
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen Adeleke, Pelumi Olajengbesi, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 26 ga watan Yulin 2026.
A cewar sanarwar, gwamnan da shugabannin jam’iyyar na ƙasa sun gudanar da wani taro a daren Asabar, 25 ga watan Agustan 2026 a Osogbo, babban birnin Jihar Osun.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa an tattauna batutuwan da ke fuskantar jam’iyyar a yayin taron.
Accord ta goyi bayan ayyukan Tinubu
Shugabannin jam’iyyar sun ce yana da muhimmanci gwamnatin Tinubu ta kammala dukkan ayyukan tituna da ababen more rayuwa da ta fara.
Sun ambaci titin Lagos-Calabar Coastal Road da babbar hanyar Sokoto-Badagry a matsayin wasu daga cikin manyan ayyukan da ya kamata a kammala.
An tattauna zaben gwamnan Osun
An kuma tattauna batutuwan da suka shafi zaɓen gwamnan Osun da za a gudanar a watan Agustan 2026.
Shugabannin jam’iyyar sun yi gargaɗi kan tashin hankali, tsoratarwa, magudin zaɓe da kuma amfani da jami’an tsaro wajen cin zarafin mambobin Accord a Jihar Osun.

Source: Twitter
Manyan shugabanni sun halarci taron
Daga cikin shugabannin jam’iyyar na ƙasa da suka halarci taron akwai shugaban jam'iyyar na ƙasa, Maxwell Mgbudem; mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Maryam Sale; sakatare na ƙasa, Ajaja Abiola Adebukola.
Sauran shugabannin da suka halarci taron sun hada da ma’aji na ƙasa, Abdulazeez Oyeniyi Salaudeen; sakataren shirya ayyuka na ƙasa, Ibe Thankgod; da sakataren yaɗa labarai na ƙasa, Omorogbe Joseph, da sauran su.
Shugabannin jam’iyyar na jihohi daga sassa daban-daban na ƙasar ma sun halarci taron da aka gudanar.
An yi hasashen nasarar Tinubu a zaben 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani fasto ya yi hasashen dan takarar da zai samu nasarar lashe zaben shekarar 2027.
Prophet Elijah Bamidele ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ke kan kujerar mulki, zai ci gaba da rike kujerar shugaban kasa a Najeriya.
Elijah Bamidele, wanda shi ne shugaban Christ House of Prayer and Deliverance Ministry, ya ce hasashensa ya nuna cewa Shugaba Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

