An Tsare Tsohon Jami'in DSS a Gidan Kaso kan Zargin Alaka da Kungiyar Ta'addanci
- Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gurfanar da tsohon jami'inta a kotun tarayya bisa zargin shiga IPOB da kuma tallafa wa kungiyar da aka haramta a Najeriya
- Ana zarginsa da yada sakonni a kafafen sada zumunta domin jan hankalin jama'a su goyi bayan IPOB, lamarin da DSS ta ce ya saba dokokin yaki da ta'addanci
- Wanda ake zargin ya musanta dukkan tuhume-tuhumen, yayin da kotu ta tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje tare da sanya ranar 29 ga Oktoba domin fara shari'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon jami'inta a gaban kotu kan zargin goyon bayan kungiyar IPOB.
An gurfanar da Nwaogu Ihechimere Ezeakolam, a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin alakanta kansa da kungiyar IPOB, wadda gwamnatin Najeriya ta haramta tare da ayyana ta a matsayin kungiyar ta'addanci.

Kara karanta wannan
Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun yaba wa Tinubu duk da matsalolin tsaro da ake ciki

Source: Getty Images
An gurfanar da shi a gaban Mai Shari'a Mohammed Umar kan tuhume-tuhume hudu da Daraktan Gurfanar da Masu Laifi na Tarayya, Rotimi Oyedepo, SAN, ya shigar, cewar Tribune.
DSS ta ce Ezeakolam ya bayar da goyon baya da taimako ga IPOB, abin da ta ce ya saba da Dokar Yaki da Hana Ta'addanci ta shekarar 2022.
Haka kuma ana zarginsa da shiga kungiyar IPOB duk da saninsa cewa gwamnati ta haramta kungiyar.
DSS ta ce wannan laifi ne da ke karkashin sashe na 25 na Dokar Yaki da Hana Ta'addanci ta shekarar 2022.
Bugu da kari, hukumar ta zarge shi da wallafa sakonni a kafafen sada zumunta da nufin jawo hankalin mutane su goyi bayan IPOB.
DSS ta ce hakan ya saba da sashe na 26 na dokar yaki da ta'addanci.
A wani karin zargi kuma, an ce tsohon jami'in ya wallafa sakonni a kafafen sada zumunta domin ingiza manufofin IPOB.
DSS ta ce wannan ya saba da sashe na 18 na Dokar Hana Laifukan Intanet ta shekarar 2015 da aka yi wa kwaskwarima.
Da aka karanta masa tuhume-tuhumen a kotu, Ezeakolam ya musanta dukkan laifukan da ake zarginsa da aikatawa. Lauyar DSS, Memunat Oladunjoye, ta bukaci kotu ta sanya ranar fara shari'a.
Sai dai lauyan wanda ake kara, Godfirst Maduka, ya nemi a ba shi lokaci domin shigar da bukatar beli. Mai shari'a ya ce ana iya shigar da bukatar a kowane lokaci, sannan ya sanya ranar 29 ga Oktoba domin fara shari'a tare da ba da umarnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na Kuje har sai an yanke hukunci kan bukatar belinsa.
A cewar takardar tuhume-tuhumen, ana zargin Ezeakolam ya rika amfani da intanet da shafukansa na sada zumunta tsakanin shekarun 2025 da 2026 domin yada bayanai da kuma bayar da goyon bayan da DSS ta ce yana taimaka wa IPOB.
Har ila yau, takardar ta ce ya shiga kungiyar IPOB a Abia tare da wallafa sakonnin da aka tsara domin rinjayar jama'a su mara wa kungiyar baya.

Kara karanta wannan
Malamin addini ya tubure kan dokar gwamnatin Tinubu na hana wa'azi, ya sha alwashi
DSS ta kuma ce ya wallafa bayanan da suka taimaka wajen ingiza manufofin kungiyar, lamarin da ya sa aka gurfanar da shi bisa dokokin yaki da ta'addanci da na hana laifukan intanet.
DSS ya bankado shirin Boko Haram
An ji cewa Hukumar DSS ta yi gargadin cewa ‘yan Boko Haram na shirin kai manyan hare-hare a ƙananan hukumomin Michika da Askira-Uba.
Rahoton ya ce ‘yan ta’addan na shirin yin garkuwa da manyan jami’an gwamnati, hakimai, fastoci da mazauna yankunan.
DSS ta buƙaci jami’an tsaro da masu gadin dazuka su ƙara tsaurara matakan tsaro domin hana hare-haren.
Asali: Legit.ng
