VeryDarkMan: Dan Tiktok Ya Gindaya Sharuddan Amsa Gayyatar 'Yan Sanda

VeryDarkMan: Dan Tiktok Ya Gindaya Sharuddan Amsa Gayyatar 'Yan Sanda

  • Martins Otse da aka fi sani da VeryDarkMan ya ce a shirye yake ya amsa gayyatar 'yan sanda kan zargin da ya yi wa AIG Moshood Jimoh
  • Lauyansa, Deji Adeyanju, ya ce dole a gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci domin tabbatar da amincewar jama'a
  • VeryDarkMan ya bukaci a ba kungiyar lauyoyi ta Najeriya da kungiyoyin fararen hula damar sa ido a yayin tambayoyin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shahararren mai tasiri a kafafen sada zumunta, Martins Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, ya bayyana sharuddan da ya ce dole ne a cika kafin ya amsa gayyatar rundunar 'yan sandan Najeriya.

Rundunar 'yan sanda ta gayyaci VeryDarkMan ne dangane da zarge-zargen da ya yi wa Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan Sanda (AIG) mai kula da shiyya ta biyu (Zone 2), Moshood Jimoh.

Kara karanta wannan

'Dan TikTok a Najeriya ya jefa shugaban 'yan sanda a matsala, an fara bincike

Verydarkman zai amsa gayyatar 'yan sanda
Martins Otse wanda aka fi sani da VeryDarkMan da AIG Jimoh Hoto: Verydarkman
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da lauyansa, Deji Adeyanju, ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Laraba, 5 ga watan Agustan 2026.

VeryDarkMan ya ce a shirye yake ya bayyana gaban masu bincike, amma ya dage cewa dole ne a gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci domin jama'a su gamsu da tsarin.

Dalilin gayyatar VeryDarkMan

Lamarin ya biyo bayan gayyatar da rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi wa VeryDarkMan domin ya bayyana a gaban Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar (FCID) da ke Abuja.

An bukace shi ne ya gabatar da hujjojin da ke goyon bayan zarge-zargen da ya yi kan AIG mai kula da Zone 2 Command.

VeryDarkMan zai bayar da hadin kai

A martanin da tawagar lauyoyinsa ta fitar, an bayyana cewa VeryDarkMan bai taba kin amsa duk wata sahihiyar gayyata ta bincike ba.

Sanarwar ta ce:

"Wanda muke wakilta ya yaba da matakin da rundunar 'yan sandan Najeriya ta dauka na fara bincike kan batutuwan da ya gabatar, kuma ya sake jaddada cewa a shirye yake ya ba da cikakken hadin kai."

Kara karanta wannan

An tsinci gawar malami a yashe, an ce wasu ne suka daɓa masa wuka har lahira

"Domin kauce wa shakku, wanda muke wakilta bai taba kin amsa duk wata gayyata ta sahihin bincike ba. A koyaushe yana shirye, yana da niyya kuma yana nan a shirye domin amsa duk wata gayyata da rundunar 'yan sanda ta yi masa bisa doka."

Sharuɗɗan da ya gindaya

Duk da amincewarsa da binciken, lauyoyin VeryDarkMan sun ce yanayin wannan batu na bukatar a gudanar da shi cikin gaskiya da rikon amana saboda irin hankalin da jama'a suka ba lamarin da kuma matsayin babban jami'in da ake zargi.

Daga cikin sharuddan da suka gabatar akwai:

  • A ba wakilan Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) damar halartar zaman binciken.
  • A gayyaci kungiyoyin fararen hula da sauran masu sa ido masu zaman kansu domin su sanya ido kan tambayoyin.
  • A bar lauyansa ya raka shi kuma ya kasance tare da shi daga farkon binciken har zuwa karshensa.
Yan sanda sun gayyaci Verydarkman
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Batun 'yan sandan jihohi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba 'yan Najeriya kan batun kafa 'yan sandan jihohi.

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa tsarin ’yan sandan jiha da ake shirin kafawa zai kunshi matakan kariya da za su hana gwamnonin jihohi yin amfani da rundunar ba bisa ka’ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng