'Yadda Aka Samu Kudin Kamfen din Buhari a Zaben Shekarar 2015'
- Babachir Lawal ya ce Bola Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen daukar nauyin yakin neman zaben Muhammadu Buhari a 2015
- Tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya ce Tinubu ya taimaka wajen samar da isassun kudaden gudanar da yakin neman zaben APC
- Babachir Lawal ya ce Tinubu ya biya kudin jirgin sama mai zaman kansa da kuma kwararrun masu ba da shawara kan siyasa daga Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya yi magana kan yakin neman zaben Marigayi Muhammadu Buhari a 2015.
Babachir Lawal ya ce Shugaba Bola Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen daukar nauyin yakin neman zaben marigayi tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a 2015.

Source: Facebook
Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya bayyana hakan ne a wata hira da Symfoni TV, wadda aka wallafa a ranar Asabar, 25 ga watan Yulin 2026.
Babachir ya tuna da yadda ya shiga yakin neman zaben Buhari, yana mai cewa Tinubu ne ya taimaka da kudade a lokacin da kwamitin yakin neman zaben ya fuskanci matsalar samun kudin gudanar da kamfen.
Ya ce marigayi tsohon shugaban kasar bai cika jin dadin tattauna batutuwan kudi ba, kuma ba kasafai yake shiga tattaunawar da ta shafi neman kudin yakin neman zabe ba.
Buhari bai damu da kudi ba
“Bayan Buhari ya lashe tikitin takara, an samu matsalar kudin yakin neman zabe. Buhari ba mutum ne mai sha’awar kudi ba. Duk lokacin da aka fara magana kan kudi, Buhari sai ya kalli silin."
“Duk lokacin da aka ce shugabanni su bayar da wani abu, Buhari sai ya yi kamar bai ji ba. Kudi ba abin da yake jin dadin tattaunawa ba ne ko kadan.”
Babachir Lawal ya ce shi da Timipre Sylva, tsohon gwamnan Bayelsa, sun tuntubi wani attajirin dan kasuwa da ake ganin yana goyon bayan takarar Buhari, domin neman taimakon kudin yakin neman zabe.
Ya ce sun gana da dan kasuwar ne a cikin jirgin ruwansa mai zaman kansa, bayan dan kasuwar ya ki ganinsu a bainar jama’a saboda sun fara shahara a matsayin manyan jiga-jigan yakin neman zaben Buhari.
Babachir ya ce dan kasuwar ya amince zai taimaka wa yakin neman zaben, amma daga bisani Sylva ya fara fargaba bayan wani dan sanda ya gaishe shi da harshen Ijaw bayan ganawar.
Jonathan ya ji labarin ganawar
Tsohon gwamnan Bayelsa ya ji tsoron cewa za a kai rahoton ganawar ga Shugaba Goodluck Jonathan na lokacin.
Babachir Lawal ya ce fargabar Sylva ta tabbata, inda ya bayyana cewa:
“Ya ce wannan sajan din dan Bayelsa ne kuma dan uwan Goodluck ne. Duk lokacin da Goodluck yake son samun wani bayani a kanka, shi ne ake tura maka. Don haka, wannan ganawar da muka yi da dan kasuwar da tuni ta isa kunnen shugaban kasa. Kuma haka ta faru."
Ya yi ikirarin cewa lokacin da suka koma Abuja, tuni an tuntubi dan kasuwar, lamarin da ya sa kusan ba zai yiwu yakin neman zaben ya samu taimakon kudinsa ba.
“Daga wannan rana, babu wani attajiri da zai daga mana waya,” in ji shi.
Babachir ya nemi taimakon Tinubu
A yayin da matsalar kudi ke kara tsananta, Babachir Lawal ya ce ya juya ga Tinubu domin neman taimako.
“Saboda haka, na je wurin Bola. Na ce, ‘Oga, za ka iya taimaka mana a wannan lamari?’ Kuma ya taimaka. Ta hanyarsa ne muka samu isassun kudaden gudanar da yakin neman zaben,” in ji shi.
Ya ce Tinubu da kansa ya dauki nauyin wasu muhimman bangarorin yakin neman zaben jam’iyyar APC, ciki har da yakin neman zaben Yemi Osinbajo na kujerar mataimakin shugaban kasa, wanda daga bisani ya yi shekaru takwas a matsayin mataimakin Buhari.
Ya yi ikirarin cewa Tinubu ya samar da jirgin sama mai zaman kansa domin ayyukan yakin neman zabe, tare da biyan kudin kwararrun masu ba da shawara kan siyasa daga Amurka da suka gudanar da bincike da sauran ayyukan kwararru na kamfen.
“Sun zo suka sauya kamfen dinmu. Na san kudin da ya biya su ya haura kwatankwacin Naira biliyan biyu,” in ji shi.

Source: Facebook
Tinubu ya biya manyan kudaden kamfen
Babachir Lawal ya kuma ce Tinubu da kansa ya biya wasu manyan kudaden yakin neman zaben ba tare da tura kudaden ta tsarin hukumance na kamfen ba.
“Idan akwai bukatar kashe kudi, komai girman kudin, bai zo ofishin kamfen ba. Daga aljihunsa yake kashewa,” in ji shi.
Ya kara da cewa masu ba da shawara da Tinubu ya dauka sun sauya yadda jama’a ke kallon Buhari a lokacin yakin neman zaben.
“Kun lura da yadda kwatsam Buhari ya fara sanya kwat. Kwatsam kuma ya fara sanya kayan Yarbawa. Mutanen da Bola ya kawo sun sauya alkiblar yakin neman zaben,” in ji shi.
Gowon ya kare Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban mulkin soja, Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya kare salon mulkin marigayi Muhammadu Buhari.
Tsohon shugaban kasar ya ce marigayi Buhari ya jagoranci Najeriya ba tare da nuna son kai ga wani yanki ba.
Asali: Legit.ng



