Zaben 2027: Takarar Pantami Ta Kara Karfi yayin da APC Ta Samu Koma Baya a Gombe

Zaben 2027: Takarar Pantami Ta Kara Karfi yayin da APC Ta Samu Koma Baya a Gombe

  • Shugaban APC na mazabar Pantami da ke jihar Gombe, Alhaji Bala Salihu Ngalda, ya fice daga jam'iyyar zuwa PDP mai adawa
  • Hakazalika lauyan jam'iyyat APC na mazabar Pantami, Babangida Atiku Gololo, shi ma ya yi murabus tare da sauya sheka
  • Lamarin na zuwa ne yayin da PDP ke ci gaba da karɓar masu sauya sheka a jihar Gombe yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na mazabar Pantami a jihar Gombe, Alhaji Bala Salihu Ngalda, ya sauya sheka.

Shugaban na APC tare da Lauyan jam'iyyar na mazabar, Babangida Atiku Gololo, sun sanar da murabus daga mukamansu tare da sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai adawa.

APC ta samu tagomashi a Gombe
Tsohon shugaban APC da lauyan jam'iyyar a mazabar Pantami Hoto: Pantami TV concept
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wasikun ficewarsu daga PDP zuwa jam'iyyar PDP wadda wadanda Legit Hausa ta samu a ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

ADC ta kalubalanci Tinubu ya ziyarci Zamfara bayan mummunan hari

Sun bayyana hakan ne a ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2026 inda suka tabbatar da ficewarsu daga APC da kuma komawa PDP.

Meyasa suka fice daga APC zuwa PDP?

"Na rubuto wannan wasika domin sanar da murabus dina daga shugaba da kuma mamba na jam'iyyar APC a mazabar Pantami nan take."
"Daukar wannan matakin ya biyo bayan tattaunawa da iyalaina kuma ina fatan za fahimta tare da mutunta hakan."

- Alhaji Salisu Bala Ngalda

Alhaji Salisu Bala Ngalda ya kuma nuna godiyarsa ga jam'iyyar a matakin karamar hukuma, jiha da kasa kan damar da aka ba shi ta shugabanci.

An yi wa APC godiya

Hakazalika ya kuma nuna godiyarsa ga gwamnatin jihar Gombe saboda goyon baya da hadin kan da ta ba shi a lokacin mulkinsa.

Ya kara da cewa duk da cewa ya raba gari da jam'iyyar APC, zai ci gaba da mutunta ta tare da yi mata fatan alheri.

Shi ma a nasa bangaren lauyan APC na mazabar Pantami, Babangida Atiku Gololo, ya bayyana cewa ya fice daga cikin jam'iyyar ne bayan ya yi shawara da iyalansa.

Kara karanta wannan

Bayan shekara a APC, Sanata ya koma tsohuwar jam'iyyarsa

Babangida Atiku Gololo ya kuma bukaci a mutunta wannan shawara da ya yanke ta raba gari da jam'iyyar APC mai mulki a jihar Gombe.

PDP ta samu tagomashi a jihar Gombe
Tsohon lauyan APC a mazabar Pantami, Babangida T Gololo Hoto: Pantami tv concept
Source: Facebook

PDP na ci gaba da karɓar masu sauya sheka

Sauya shekar tasu na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar PDP ke ci gaba da samun sabbin mambobi daga jam'iyyu daban-daban a jihar Gombe.

Lamarin na nuni da ci gaba da sauyin yanayin siyasa a jihar, yayin da jam'iyyun siyasa ke ci gaba da fafatawa wajen ƙara yawan mambobinsu.

Pantami ya samu goyon baya a Gombe

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai neman takarar gwamnan Gombe a karkashin jam’iyyar PDP, Mohammed Manu Malala, ya bayyana goyon bayansa ga Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

Mohammed Manu Malala, wanda tsohon babban sakatare ne a jihar Gombe, ya bayyana goyon bayansa ne yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng