Badakalar PFIPC: Majalisar Wakikai Ta ba IGP Umarni kan Adeniyi Adeyemi
- Wani kwamitin Majalisar Wakilai ya umurci IGP Olatunji Disu ya gabatar da Adeyemi Adeniyi a gabansa ranar Laraba
- Kwamitin na binciken yadda PFIPC ta samu ofis da kuma N1.32bn a kasafin kudin 2026 duk da cewa ba a kafa ta bisa doka ba
- ’Yan sanda sun tabbatar da cewa an shigar da Adeyemi kara mai tuhume-tuhume takwas a gaban Babbar Kotun Tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kwamitin Majalisar Wakilai da ke binciken ayyukan hukumar PFIPC mai cike da ce-ce-ku-ce ya ba babban sufeton ’yan sanda, Olatunji Disu, umarni.
Kwamitin ya umarci Olatunji Disu ya gabatar da wanda ke ikirarin shi ne shugaban hukumar PFIPC, Adeyemi Adeniyi, a gabansa a ranar Laraba, 29 ga watan Yulin 2026.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce an bayar da umarnin ne ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2026 yayin da aka ci gaba da zaman binciken kwamitin a harabar Majalisar Dokoki ta Kasa da ke Abuja.
Wane umarni majalisa ta ba IGP?
Mataimakin kwamishinan ’yan sanda, Bashir Abdullahi, wanda ya wakilci IGP a zaman, ya bayyana a gaban kwamitin, inda aka umurce shi da tabbatar da cewa Adeyemi ya bayyana a gaban kwamitin kafin karfe 12:00 na rana a ranar Laraba domin taimaka wa ’yan majalisar wajen ci gaba da binciken ayyukan hukumar.
Kwamitin na binciken yadda PFIPC, duk da cewa ba a kafa ta bisa doka ba, ta samu ofishin aiki a Phase III na harabar sakatariyar tarayya da ke Abuja, tare da samun rabon N1.32bn a cikin kasafin kudin 2026.
An bayar da umarnin ne bayan rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da wasu muhimman bangarorin binciken laifin da take gudanarwa, ciki har da koke-koken da Ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya shigar, inda aka zargi Adeyemi da yin ikirarin karya cewa shi ne shugaban PFIPC.
Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, ya ce bayyanar Adeyemi a gaban kwamitin ta zama wajibi saboda girman zarge-zargen da kuma cibiyoyin da lamarin ya shafa.
Meyasa ake son a kawo Adeyemi?
“A fili wannan kwamitin na bukatar wanda ake zargi da zama DG ya bayyana a gaban kwamitin. Sunayen mutane na ciki. Mutuncin mutane na ciki. Sunayen cibiyoyi na ciki. Mutuncin cibiyoyi na ciki."
“Ba wani zabi ba ne yanzu. Muna bukatarsa a nan domin ya tabbatar mana da wasu takardu ta hanyar da ba za ta kawo cikas ga bincikenmu ba, domin mu samu damar gabatar da rahotonmu a kan lokaci,” in ji Gagdi.
Daga nan ne kwamitin ya umurci magatakardansa da ya sanar da babban sufeton ’yan sanda a hukumance game da matsayar da aka cimma, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
"Kwamitin ya yanke shawarar cewa babban sufeton ’yan sanda na Tarayyar Najeriya ya gabatar da Mista Adeyemi ranar Laraba da karfe 12:00 na rana. Wannan shi ne hukuncin kwamitin.”
- Yusuf Gagdi

Source: Facebook
’Yan sanda sun shigar da kara
Tun da farko, ACP Abdullahi ya sanar da ’yan majalisar cewa duk da cewa bincike na ci gaba, ’yan sanda sun riga sun shigar da tuhume-tuhume takwas a kan Adeyemi a gaban Babbar Kotun Tarayya.
“Rundunar ’yan sandan Najeriya ta binciki wani bangare na wannan batu a karshen shekarar da ta gabata, sannan ta shigar da tuhume-tuhume takwas a gaban Babbar Kotun Tarayya. Shari’ar na ci gaba,” in ji shi.
Dalilin kafa hukumar PFIPC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar PFIPC, Adeniyi Adeyemi Matthew, wadda ake takaddama a kanta ya bayyana dalilin kafa ta.
Adeyemi ya bayyana cewa ya kafa hukumar ne saboda kishin da yaye yi wa Najeriya domin jawo masu zuba hannun jari.
Asali: Legit.ng


