Abin Boye Ya Fito: An Gano Hanyar da Aka Kafa Ma'aikatar Bogi ta PFIPC
- An samu bayanai kan hanyar da aka bi wajen kafa hukumar bogi ta PFIPC da ke ta takaddama a kanra
- Akanta-Janar na Tarayya Shamseldeen Ogunjimi ya ce ba a taɓa sakin ko sisi daga cikin kuɗaɗen gwamnati ga hukumar ba
- An nemi tallafin kafa hukumar na N27.4bn, amma aka yi watsi da buƙatar saboda babu tanadin a kasafin kuɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Binciken da Majalisar Wakilai ke gudanarwa kan ayyukan hukumar PFIPC ya ɗauki sabon salo bayan bayyanar Akanta-Janar na Tarayya, Shamseldeen Ogunjimi.
Akanta-Janar na tarayya ya bayyana cewa an yi amfani da wasiƙar fadar shugaban ƙasa ta bogi wajen samun amincewar hukuma ga “hukumar bogin”

Source: Facebook
Ogunjimi ya bayyana hakan ne a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar da ke binciken yadda aka kafa hukumar da kuma ayyukanta a ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta hango kura kurai a kalaman Obi, ta yi masa zazzafan martani
Ya ce Ofishin Akanta-Janar ya yi aiki ne bisa wata wasiƙa da ta yi kama da sahihiyar wasiƙar fadar shugaban ƙasa, wadda ta nemi a samar wa PIFPC lambar gudanarwa domin sauƙaƙa tsara kasafin kuɗi, lissafin kuɗi da rahoton harkokin kuɗi.
Sai dai bincike ya nuna daga baya cewa wasiƙar ba ta fito daga fadar shugaban ƙasa ba, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.
Yadda aka fara hulɗa da hukumar
Yayin gabatar da rahotonsa, Ogunjimi ya ce Ofishin Akanta-Janar ya fara hulɗa da hukumar da ake zargin tun a watan Nuwamba 2024.
A cewarsa:
"Wata wasiƙa mai kwanan wata 7 ga Nuwamba, 2024, wadda ke ɗauke da lambar tuntuɓar fadar shugaban ƙasa, ta nemi a samar da lambar gudanarwa ga PFIPC domin sauƙaƙa harkokin kasafi, lissafin kuɗi da rahoton harkokin kuɗi”
Ya bayyana cewa bisa tsarin da aka saba bi, “Ofishin Akanta-Janar ya aiwatar da buƙatar, ya samar da lambar gudanarwar sannan ya sanar da fadar shugaban ƙasa cewa an amince da ita”, tare da aika kwafi zuwa Ofishin Akanta-Janar na Tarayya
Bayan wannan amincewa, ofishin ya karɓi wasu buƙatu daga hukumar, ciki har da neman matsayin gudanar da lissafin kuɗaɗenta da kanta, tura ma’aikata, buɗe asusun TSA da asusun ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje, da kuma neman amincewar tallafin kuɗi.
Ba a saki kuɗin gwamnati ba
Sai dai Ogunjimi ya jaddada cewa duk da cewa an gudanar da wasu matakan gudanarwa, ba a taɓa sakin kuɗin gwamnati ga hukumar ba.
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta nemi tallafin kafa ta na N27.4bn, amma aka yi watsi da buƙatar saboda babu tanadin kasafi na irin wannan kashe kuɗi.
Akanta-Janar ɗin ya ƙara da cewa duk da cewa CBN ya buɗe wa hukumar asusun ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje guda biyu domin karɓar kuɗaɗen da za su shigo, asusun ba su taɓa fara aiki ba saboda hukumar ta gaza cika sharuddan da hukumomin da abin ya shafa suka gindaya kafin bude su.

Source: Facebook
An yi amfani da wasiƙar bogi
'Yan majalisar sun nuna damuwa kan yadda hukumar da ake zargin ta iya tsallake matakai daban-daban na tsarin mulkin gwamnati ba tare da an gano abin da ke faruwa ba.
A yayin amsa tambayoyin su, Ogunjimi ya bayyana abin da mambobin kwamitin suka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan bayanan da aka samu a zaman binciken.
“Wasiƙar da ofishin ya karɓa an rubuta ta cikin girmamawa kamar ta fito daga fadar shugaban ƙasa. Amma wannan wasiƙar ba ta taɓa fitowa daga fadar shugaban ƙasa ba,” in ji shi
Majalisa ta bukaci a kawo Adeyemi
A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin Majalisar Wakilai da ke bincikar badakalar PFIPC, ya mika bukatarsa ga babban sufeton 'yan sanda.
Kwamitin ya umarci IGP, Olatunji Rilwan Disu da ya gabatar mata da mutumin da ke ikirarin shugabantar hukumar, Adeniyi Adeyemi.
Asali: Legit.ng

