Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya tuna baya kan abubuwan da suka faru da shi kafin ya dare kujerar mulki. Ya bayyana cewa an ba shi kyautar kudi.
Kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa tana da sharadin da take son a cika kafin ta kulla yarjejeniya da Amurka kan yakim Gabas ta Taakiya.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin mutanen jihar.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tura sakon ta'aziyyabayan ya samu sakon rasuwar tsohon kwamishinan albarkatun ruwa da raya karkara, Dr. Mahmoud Baffa.
Tsagin jam'iyyar ADC karkashin jagorancin Nafiu Bala Gombe, ya bayyana dan takarar shugaban kasa a zaben 2027. An zabe shi ne ta hanyar bin tsarin maslaha.
Tsohon Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, ya yi tsokaci kan rahotannin da ke cewa ya soki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayan rasa tikitin APC a jihar Bauchi.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Zamfara sun samu nasarar yin caraf da wani jagoran 'yan bindiga. 'Yan sandan sun kuma cafke wasu 'yan bindiga da dama.
Matatar Dangite da ke jihar Legas a Najeriya ta rage farashin kowace litar man fetur a Najeriya saboda saukin da aka samu a farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Jam'iyyar APM ta tabbatar da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a matsayin 'dan takarar shugaban a zabe mai zuwa, ta mika masa tutar jam'iyya a hukumance
Manyan Labarai A Yau
Samu kari