Fashola: Tsohon Gwamna Ya Fadi Dalilin Kin Sukar Gwamnatin Tinubu

Fashola: Tsohon Gwamna Ya Fadi Dalilin Kin Sukar Gwamnatin Tinubu

  • Tsohon gwamnan Legas, Babatunde Raji Fashola ya ce yana da damar kai tsaye wajen tuntubar Shugaba Bola Tinubu
  • Fashola ya ce shugaban ƙasar kan nemi shawararsa kan yadda za a inganta mulki gabanin zaɓen 2027
  • Tsohon Ministan ayyuka da gidaje na Najeriya ya kuma bayyana cewa ba shi da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Tsohon gwamnan Jihar Legas kuma tsohon Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya yi magana kan rashin sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Fashola ya bayyana cewa ya fi son ba Shugaba Bola Tinubu shawara a sirrance maimakon ya riƙa sukar gwamnatinsa a bainar jama’a.

Fashola ya ce ba zai soki Tinubu a fili ba
Tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Raji Fashola Hoto: Babatunde Raji Fashola
Source: Facebook

Fashola ya bayyana hakan ne yayin wata hira da TVC News ranar Laraba, 22 ga watan Yulin 2026 lokacin da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya fi mayar da hankali wajen yin shiru kan ayyukan gwamnatin Tinubu a bainar jama’a.

Kara karanta wannan

'Yabon Trump ya nuna aikinmu ya na kyau': Fadar shugaban kasa

Me yasa Fashola bai sukar Tinubu?

Ya ce Shugaba Tinubu kan nemi ra’ayinsa a kai a kai kan harkokin mulki da wuraren da ake buƙatar ingantawa yayin da gwamnatin ke shirin tunkarar babban zaɓen 2027.

Da yake bayyana dalilin da ya sa ba ya tattauna irin waɗannan batutuwa a talabijin, Fashola ya ce ya fi ganin dacewar isar da ra’ayinsa kai tsaye ga shugaban ƙasar.

“Yau ya kira ni, ya ce, ‘Yau, ka gano wani fanni guda ɗaya da gwamnatina dole ta inganta yayin da muke ƙirga kwanaki zuwa 2027. Me za ka ba ni shawara?’ To, zan zo na ba shugaban ƙasa shawara a talabijin ne? Na riga na gaya wa kaina cewa ba zan yi hakan ba,” in ji Fashola

Tsohon ministan ya ce ya riga ya ba shugaban ƙasar shawara kan wasu batutuwa, yana mai cewa kiyaye wannan hanyar tuntuba ta sirri ta fi masa muhimmanci fiye da yin kalamai a bainar jama’a.

Kara karanta wannan

"Ya fi su": Gwamna Sule ya fadi fannin da Tinubu ya yi wa Atiku, Obi fintinkau

“Yana jin abin da nake faɗa, kuma idan na bukaci ganinsa, na ba da shawara kan wasu abubuwa. Ina ganin dole ne mu ci gaba da buɗe wannan hanya. Ba ni da niyyar ba shi shawara a talabijin,” in ji shi

Fashola ya ce gwamnati na kokari

Da aka tambaye shi ko gwamnatin ta samu wasu gibi ko wuraren da ba ta kula da su ba bayan kusan shekaru uku a mulki, Fashola ya yi watsi da hakan, yana mai cewa damar da yake da ita ta tuntubar shugaban ƙasa kai tsaye ta sa sukar gwamnati a bainar jama’a ba ta zama dole ba.

“Babu wasu wuraren da wannan gwamnati ba ta taba ba. Ba za ka riƙa ihu ga mutumin da yake jin abin da kake faɗa ba,” in ji shi

Mai tambayoyin ya ce ‘yan Najeriya da dama sun yi tsammanin Fashola zai rika yin magana kan manyan batutuwan ƙasa bayan ya bar mukamin gwamnati, amma tsohon gwamnan Legas ya ce salon da yake bi bai canza ba.

Fashola ya yi magana kan gwamnatin Tinubu
Babatunde Raji Fashola na jawabi a wajen taro Hoto: Babatunde Raji Fashola
Source: Facebook

Fashola bai da burin yin takara

Fashola ya kuma yi watsi da jita-jitar cewa zai iya tsayawa takarar shugaban ƙasa a nan gaba, yana mai cewa ba shi da irin wannan buri.

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu sun mayar wa Kwankwaso martani kan tikitin Musulmi Musulmi

Da aka tambaye shi ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa, sai ya amsa da cewa, “A’a.”

Lokacin da mai tambayoyin ya ƙara matsa masa da tambayar, Fashola ya amsa cikin murmushi:

“Shugaban ƙasar me? Ni shugaba ne a gida.”

Trump ya yabawa Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya aiko da wasika ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Shugaba Trump ya yabawa Tinubu kan kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen yakar 'yan ta'adda da masu tayar da kayar baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng