Turawa Sun Shiga Tashin Hankali: Fiye da Mutane 5,700 Sun Mutu a Kasar Faransa

Turawa Sun Shiga Tashin Hankali: Fiye da Mutane 5,700 Sun Mutu a Kasar Faransa

  • Hukumar lafiya ta bayyana cewa akalla mutane 5,764 sun mutu fiye da yadda aka saba sakamakon mummunar guguwar zafi da ta afku a watan Yuni
  • Yankin babban birnin kasar ya fi fuskantar asarar rayuka, yayin da asibitoci da cibiyoyin ajiye gawa suka fuskanci matsin lamba
  • Hukumar ta ce guguwar zafin ita ce mafi muni tun shekarar 2003, lokacin da irin wannan bala'i ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 15,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Faransa - Hukumar Lafiyar Jama'a ta Faransa ta bayyana cewa akalla mutane 5,764 sun mutu fiye da yadda aka saba sakamakon tsananin zafi da ya afku tsakanin ranar 17 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yulin 2026.

Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa mutane 21,674 ne suka mutu a yankunan da guguwar zafin ta shafa, yayin da a yanayi na al'ada ana sa ran mutuwar mutane 15,910 kacal.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun birkita kauyen Sokoto da harbi, sun sace sama da mutum 50

Rahoto ya nuna cewa dattawa fiye da 5,700 ne suka samu a watan Yunin 2026 a Faransa
Wata mata rike da robar ruwa yayin da ake tsananin zafi a Turai. Hoto: fcafotodigital via Getty Images
Source: Getty Images

Tura masu yawa sun mutu a Faransa

Hukumar ta bayyana cewa karin mutuwar ya kai kashi 36 cikin 100 fiye da yadda aka saba, lamarin da ya sa wannan guguwar zafi ta zama mafi muni tun shekarar 2003, in ji rahoton APC News.

A shekarar 2003, wani irin wannan yanayi ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 15,000 a Faransa.

Rahoton ya nuna cewa sama da rabin mutuwar ta faru ne tsakanin ranar 25 zuwa 27 ga watan Yuni, lokacin da zafin ya kai kololuwa.

Zafin da ya karya tarihi a Faransa

Faransa ta samu kwanaki mafi zafi a tarihinta a ranar 24 da 25 ga watan Yuni, inda matsakaicin zafin kasar ya kai digiri 30 na ma'aunin Celsius.

A wurare da dama, zafin ya haura digiri 40 na Celsius, yayin da dararen ma suka kasance mafi zafi da aka taba samu.

Hukumar ta ce kusan daukacin al'ummar kasar sun fuskanci matsanancin zafi a lokacin da makarantu da wuraren aiki ke ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Kara karanta wannan

Ndume ya musanta zargin shiga tsakani da 'yan bindiga, ya nemi a binciki Kaigama

Yankin Paris ya fi fuskantar matsala

Rahoton ya nuna cewa yankin babban birnin Paris ne ya fi shan wahala, inda aka samu karin mutuwar mutane 1,999 fiye da yadda aka saba.

Rahoton NBC News ya nuna cewa wannan ya kai kusan kashi 80 cikin 100 sama da adadin da ake sa ran samu idan babu guguwar zafi.

Hakan ya sa cibiyoyin ajiye gawarwaki suka cika, yayin da wasu suka kasa karbar karin gawarwaki saboda rashin gurbi.

Mutuwa na ci gaba da ratsa kasashen Turai yayin da suke fuskantar tsananin zafin rana.
Wata mata tana fifita saboda tsananin zafin rana a Turai. Hoto: SimpleImages via Getty Images
Source: Getty Images

Asibitoci sun cika da marasa lafiya

Hukumar ta ce kusan rabin mutanen da suka mutu sun rasu ne a asibitoci bayan yawaitar masu fama da matsalolin da zafi ya haddasa.

Kusan kashi uku cikin goma sun mutu a gidajensu, yayin da sauran suka rasu a cibiyoyin kula da tsofaffi.

Hukumar ta bayyana cewa za ta sake sabunta alkaluman daga baya idan ta samu cikakkun bayanai.

Tsananin zafin rana a kasashen Turai

Tun da fari, mun ruwaito cewa, kasashen Turai sun samu mutuwar mutane sama da 10,000 fiye da yadda aka saba bayan tsananin zafin rana da ya mamaye yammacin nahiyar a Yuni.

Kara karanta wannan

Mai shekara 60 ya rasu bayan zuwa otel da budurwa, an samu maganin jima'i

Fiye da mutum 9,000 daga cikin wadanda suka mutu masu shekaru 65 zuwa sama ne, wadanda suka fi fuskantar barazana daga tsananin zafi.

Masana sun ce sauyin yanayi da dan Adam ke haddasawa ne ya kara tsananta zafin rana, wanda ya jawo karin mace-mace a kasashe da dama

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com