Manyan Labarai A Yau
Shugabannin APC a mazabar Odu da ke karamar hukumar Dekina a jihar Kogi sun dakatar da Sanatan Kogi ta Gabas, Jibrin Isa bisa zargin cin amanar jam'iyya.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ya buƙaci ‘yan Najeriya su yi addu’ar zaman lafiya da cigaban ƙasa yayin da ake bikin Babbar Sallah ta 2026.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi ta'aziyyar rasuwar babban malamik fannin sadarwa a jami'ar Bayero, Dr. Musa Adamu Labaran, wanda ya rasu jiya Litinin.
Jam'iyyar ADC reshen jihar Sakkwato ta bayyana tsohon mataimakin shugaban kasa, alhaji Atiku Abubakar a matsayin wanda ya samu nasara a zaben fitar da gwani.
Ma'aiatar harkokin cikin gida ta bukaci daukacin musulmin Najeriya su sa kasar a addu'a a wannan lokaci na ibada, tana mai tunatar da su muhimmancin taimakon juna.
Hukumar INEC ta shigar da kara gaban kotun daukaka kara tana neman a jingine hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na soke wani bangaren jadawalin zaben 2027.
NALPGAM ta yi gargadin cewa tashin farashin gas da ƙarancin kaya na iya haddasa matsalar ƙaranci tare da ƙara wa ‘yan Najeriya wahala. Farashin 1kg ya koma N2000.
'Yan daba sun ci karensu babu babbaka a wasu sassan jihar Kano. 'Yan daban sun kashe wasu mutane ciki har da wani sanda da ya kusa yin ritaya daga aiki.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wurin da ake gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar ADC. Sun yi awon gaba da jami'in hukumar INEC.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari