Kalu: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Tabo Batun Ware N1bn Don Sayo Kayan Kida ga Coci

Kalu: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Tabo Batun Ware N1bn Don Sayo Kayan Kida ga Coci

  • Mataimakin kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Benjamin Kalu, ya ce ba a ware naira biliyan 1 ba don sayen kayan kiɗa ga coci-coci a mazabarsa
  • Ya ce ainihin kuɗin da aka ware shi ne naira miliyan 780 bayan cire harajin VAT da sauran kuɗaɗen doka
  • Benjamin Kalu ya bayyana cewa shirin na da nufin sake ilmantar da matasa da kuma tallafa musu ta hanyar ƙungiyoyin addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mataimakin kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Benjamin Kalu, ya yi martani kan rahotannin cewa an ware N1bn ga mazabarsa don sayen kayan kida ga coci-coci.

Benjamin Kalu ya musanta rahotannin da ke cewa ofishinsa ya ware N1bn a kasafin kuɗin 2026 domin sayen kayan kiɗa ga coci-coci a mazabar tarayya ta Bende da ke jihar Abia.

Benjamin Kalu ya warware zare da abawa
Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu Hoto: Benjamin Kalu
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Levinus Nwabughiogu, ya fitar ranar Laraba, 22 ga watan Yulin 2026, Kalu ya ce ainihin kuɗin da aka ware shi ne naira miliyan 780.

Kara karanta wannan

'Yabon Trump ya nuna aikinmu ya na kyau': Fadar shugaban kasa

Mataimakin kakakin ya ce rahotannin sun ba da bayanin da ba daidai ba game da adadin kuɗin da aka ware da kuma manufar shirin.

Kalu ya fadi dalilin ware kuɗin

Ya ce bayan cire harajin VAT da sauran kuɗaɗen da doka ta tanada, kuɗin da aka ware ya kai naira miliyan 780.

A cewarsa, za a yi amfani da kuɗin ne wajen tallafa wa shirin sake ilmantar da matasa da kuma ba su tallafi kan harkokin zamantakewa, wanda za a gudanar ta hannun ƙungiyoyin da suka shafi addini.

Sanarwar ta ce za a yi amfani da kuɗin wajen sayen kayan kiɗan wa'azi da na'urorin yaɗa sauti domin tallafa wa yaƙi da munanan ɗabi'u kamar yaɗuwar miyagun ƙwayoyi, laifuffukan da suka shafi lalata da kuma munanan laifuffukan tashin hankali.

Haka kuma, shirin na da nufin ƙarfafa tarbiyya, kyawawan ɗabi'u, zaman lafiya da kuma gina halayen matasa a cikin al'ummomin yankin.

Za a tallafawa coc-coci a Bende

Kalu ya bayyana cewa mazabar tarayya ta Bende tana da mazabu 13 da kuma coci-coci sama da 200, inda ya ce kashi na farko na shirin zai shafi coci-coci 130.

Kara karanta wannan

Dangote ya dawo sayar da fetur da Naira, ya sauya farashin litar mai

“Bende tana da mazabu 13 da kuma coci-coci sama da 200. Kashi na farko na wannan tallafi zai shafi 130 daga cikin waɗannan coci-coci, wato kusan coci-coci 10 a kowace mazaba, wanda ya kai kusan Naira miliyan 5 zuwa Naira miliyan 6 ga kowace coci,” in ji shi.

Shirin zai tallafawa matasa

Mataimakin kakakin ya ce manufar shirin ita ce ƙarfafa hanyoyin da coci-coci suka riga suka kafa domin hulɗa da matasa, da nufin inganta kyawawan ɗabi'u da kuma hana munanan ayyuka, jaridar TheCable ta kawo labarin.

“Wannan shiri ba game da kayan kiɗa kaɗai yake ba. Ya shafi amfani da amintattun tsare-tsaren al'umma masu kiyaye kyawawan ɗabi'u wajen sake ilmantar da matasanmu, inganta haɗin kai da kuma tabbatar da ci gaba da koyar da ɗabi'u a dukkan mazabar,” in ji shi.
Benjamin Kalu ya ce ba a ware N1bn don coci ba
Benjamin Kalu zaune yayin zama a majalisar wakilai Hoto: Benjamin Kalu
Source: Facebook

Mataimakin kakakin ya buƙaci jama'a da kafafen yaɗa labarai su yi watsi da rahotannin da ke cewa an ware N1bn kacal domin sayen kayan kiɗa, yana mai cewa shirin wani ɓangare ne na babban ƙoƙari na inganta ci gaban matasa da kuma kyawawan ɗabi'un al'umma.

Hadimin Kalu ya yi murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya yi murabus daga mukaminsa.

Bayan murabus din nasa, tsohon hadimin na Benjamin Kalu ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar jam'iyyar LP, Chima Anyaso, gabanin babban zaben shekarar 2027 a jihar Abia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng