Gaskiya Ta Fito kan Zargin Rikici tsakanin Shugaba Tinubu da Gwamna a Najeriya

Gaskiya Ta Fito kan Zargin Rikici tsakanin Shugaba Tinubu da Gwamna a Najeriya

  • Sarkin Olugbon na Orile-Igbon, Oba Francis Alao, ya ce babu wani saɓani tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde
  • Basaraken ya kuma bayyana cewa za a warware duk wata saɓani da ke tsakaninsu idan ma akwai kafin zaɓen 2027
  • Sarkin ya kuma ce yankin Kudu maso Yamma ya kamata ya ci gaba da riƙe shugabancin ƙasa har zuwa 2031

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo, Nigeria - Sarkin Olugbon na Orile-Igbon, Oba Francis Alao, ya bayyana cewa babu wata takaddama mai girma tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin ɗan takarar gwamnan Oyo na APM, Bimbo Adekanmbi, mataimakinsa, Mufutau Open-Salawu, da sauran jiga-jigan jam’iyyar a fadarsa da ke Orile-Igbon, Ƙaramar Hukumar Surulere.

Kara karanta wannan

Fashola ya fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan yanayin lafiyar Tinubu

Makinde da Tinubu.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde lokacin da ya kai aa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ziyara a fadar Aso Rock Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

A rahoton Punch, Alao ya jaddada cewa yana da yakinin cewa shugabannin biyu za su warware duk wata matsala da ke tsakaninsu.

Tinubu ya samu sabani da Makinde?

“Babu wata matsala mai girma da ta shiga tsakanin Makinde da Tinubu, magana ce ta yan gida daya, matsalar uba da ɗa ce, za mu warware dukkan matsalolin kafin 2027,” in ji shi.

Ya kuma bayyana yakinin cewa yankin Kudu maso Yamma zai ci gaba da riƙe shugabancin ƙasar har zuwa 2031, yana mai cewa za a yi ƙoƙarin samun goyon bayan masu ruwa da tsaki a siyasa daga Arewa.

“Abu ne da ba za a sauya ba cewa Kudu maso Yamma ya kamata ya riƙe shugabancin ƙasa har zuwa 2031. Muna roƙon ’yan’uwanmu na Arewa su fahimce mu, su kuma bari mu ci gaba da kiyaye tsarin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu,” in ji shi.

Abin da Tinubu ya faɗa masa

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Da yake tuna ganawarsa da Tinubu a shekarar 2023, basaraken ya ce Shugaban ƙasar ya gaya masa cewa gwamnatinsa ta gaji kadarori da kuma basussuka, cewar Tribune Nigeria.

“Lokacin da na ziyarci Shugaba Tinubu a 2023, ya gaya mini cewa ya gaji kadarori da kuma basussuka. Yana da kyawawan tsare-tsare, amma tsare-tsarensa na kawo sauyi ne. Kafin su fara aiki yadda ya kamata, suna buƙatar lokaci,” in ji Olugbon.

Alao ya tuna da goyon bayan da ya bai wa Tinubu a takararsa ta shugaban ƙasa a 2023, inda ya ce yana cikin sarakuna kalilan a Kudu maso Yamma da suka fito fili suka bayyana goyon bayansu ga Shugaban ƙasar a lokacin.

Sarki a Oyo.
Sarkin Olugbon na Orile-Igbon, Oba Francis Alao lokacin da ya karbi bakuncin tawagar dan takarar gwamnan Oyo na APM Hoto: Oyo News
Source: Facebook

Dangantakarsa da Tinubu da Makinde

Da yake bayyana Tinubu da Makinde a matsayin mutanen da yake da kusanci da su, basaraken ya ce biyayyarsa ga Shugaban ƙasa ba ta rage kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da gwamnan Oyo ba.

“Tinubu mutum ne na kusa da ni sosai, haka ma Makinde. Tinubu mutumin kirki ne, Makinde ma mutumin kirki ne. Shugaban ƙasa ya san irin rawar da muka taka a siyasa a shekarar 2023," in ji shi.

Kara karanta wannan

"Yadda tsohon shugaban ƙasa ya roki Tinubu ya goyi bayan ɗiyarsa ta zama gwamna"

Gwamnan Oyo na hangen nasara a 2027

Kun ji cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APM kuma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce nasarorin da ya samu za su taimaka masa a 2027.

Ya bayyana ƙarin mafi ƙarancin albashi, biyan ma’aikata albashi a kan lokaci, zuba jari a fannin noma da ababen more rayuwa, da tallafa wa fitar da amfanin gona zuwa kasuwannin duniya a matsayin wasu daga cikin nasarorin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262