An Huro Wuta ga Shugaban Majalisa, Ya Samu Zabi 2 kan Kujerarsa
- ’Yan Majalisar Dokokin Jihar Ondo 21 daga cikin 26 sun rattaba hannu kan takardar tsige Kakakin Majalisar, Olamide Oladiji, kan zargin almundahanar kuɗi
- Sun zargi Kakakin da karkatar da Naira miliyan 44 da aka ware domin sake tsara kasafin kuɗin Hukumar Raya Yankunan Masu Hakar Mai ta Jihar Ondo (OSOPADEC)
- ’Yan majalisar sun ce za su tsige Kakakin idan bai yi abin da suka bukaci ya yi ba cikin mutunci da girmamawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Akure, Ondo - Rikicin da ya dabaibaye Majalisar Dokokin Jihar Ondo ya ƙara ƙamari, yayin da mafi yawan ’yan majalisar suka ba Kakakin Majalisar, Olamide Oladiji, wa’adin zuwa ranar Lahadi ya yi murabus ko kuma a tsige shi.
’Yan majalisa 21 daga cikin 26 ne suka rattaba hannu kan takardar neman tsige Kakakin bisa zargin almundahanar kuɗi.

Source: Twitter
’Yan majalisa sun ba shi wa’adi
A wata tattaunawa da jaridar The Punch ranar Laraba, 22 ga Yulin 2026, shugaban kwamitin majalisar kan yaɗa labarai, Olatunji Fabiyi, ya ce ’yan majalisar sun ƙara ba Kakakin wasu kwanaki ya yi murabus, idan ba haka ba za a tsige shi a zaman majalisar na gaba.
Ya jaddada cewa gwamnan ya shiga tsakani kan lamarin, amma ya bar ’yan majalisar su ci gaba da gudanar da ayyukansu na majalisa.
“Mun yanke shawarar cewa ya kamata shugaban majalisa ya tafi. Amma bisa shawarar shugabancin majalisar, mun ga ya kamata mu gana da Gwamna."
“Mun kai masa ƙudurin ’yan majalisar. Domin a baya, ana sukar mu ana cewa wani ne ke ɗaukar nauyinmu."
“Saboda kauce wa hakan, shugabancin majalisar ya je wurin Gwamna domin ya sanar da shi cewa wannan batu ba shi da alaƙa da shi. Abin da Kakakin ya aikata ne, kuma ba ma son ya ci gaba da jagorantar mu."
“’Yan majalisa 21 sun rattaba hannu kan tsige shi. Amma bisa shawarar shugabancin majalisar, domin kada a ga kamar mun yi gaggawar ɗaukar mataki, sai muka je wurin Gwamna."
“Gwamna ya nemi a ba shi lokaci. A kan wannan batu, ba mu da wata matsala da Gwamna. Batun ya shafi kasafin kuɗin OSOPADEC ne. An rubuta wani ƙuduri da sunan ’yan majalisa ba tare da saninmu ba. An ce ’yan majalisar sun zauna sun amince da shi, kuma an ce ƙudurinmu ne, alhali ba haka ba ne."
“Saboda haka, idan wani yana kare shi, hakan na nufin yana taimaka masa ne. Mun ba shi wa’adin zuwa ranar Lahadi. Idan bai yi murabus ba, za mu tsige shi.”
- Olatunji Fabiyi
Mai magana da yawun majalisar ya ce ’yan majalisar za su sake taro a zaman majalisa na gaba domin yanke hukunci kan makomar Kakakin.

Source: Original
An zargi Kakakin da karkatar da N44m
Jaridar The Cable ta ce a ranar Litinin, wani ɗan majalisar da ya nemi a sakaya sunansa ya zargi Kakakin da mataimakinsa da karkatar da Naira miliyan 44 da aka ware domin sake tsara kasafin kuɗin OSOPADEC.

Kara karanta wannan
A karshe, Peter Obi ya bar boye boye, ya fadi dalilin daukar Kwankwaso mataimakinsa
Ya kuma zargi Kakakin da sake tsara kasafin kuɗin hukumar ba tare da tuntuɓar sauran ’yan majalisar ba.
Kakakin ya musanta zarge-zargen
A nasa martanin, lokacin da aka tuntube shi ta waya, Kakakin Majalisar da ke fuskantar matsin lamba ya musanta zarge-zargen.
Kakakin Majalisar Dokokin ta jihar Ondo ya bayyana cewa bai san da wata takardar neman tsige shi ba.
Yunkurin tayar da bam a gidan gwamnati
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo, ya bayyana yadda jami'an tsaro suka dakatar da wani shirin tayar da bam a gidan gwamnatin jihar.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya bayyana cewa ana zargin wasu matasa ne suka yi yunkurin tayar da bam a gidan gwamnatin jihar Ondo.
Asali: Legit.ng

