Daga Karshe Dan Takarar APC a Zaben Osun Ya Yi Magana bayan Kayen da Ya Sha

Daga Karshe Dan Takarar APC a Zaben Osun Ya Yi Magana bayan Kayen da Ya Sha

  • Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji ya bukaci mambobin APC da magoya bayanta su zauna lafiya bayan sakamakon zaben gwamnan Osun
  • Oyebamiji ya ce yana mutunta matsayin hukumar zabe tare da goyon bayan matakin jam’iyyar na sake duba sakamakon zaben
  • Dan takarar na APC ya kuma bukaci gwamnati da jami’an tsaro su dakile hare-haren da ake zargin ana kai wa mambobin jam’iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala, ya bukaci mambobin jam’iyyar da magoya bayanta su zauna lafiya tare da kwantar da hankalinsu bayan sakamakon zaben.

Gwamna Ademola Adeleke, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar Accord Party, ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke Oyebamiji wanda ya samu kuri’u 444,815.

Kara karanta wannan

Isa Ashiru ya ba 'yan Najeriya shawarar abin da za su koya daga zaben gwamnan Osun

Oyebamiji ya y magana kan rashin nasararsa
Dan takarar gwamnan Osun na jam'iyyar APC, Bola Oyebamiji Hoto: Bola Oyebamiji
Source: Twitter

Oyebamiji ya yi magana a cikin sakon da ya aikewa shugabannin APC, mambobi da magoya bayan jam’iyyar a jihar a wani rubutu a shafinsa na Facebook ranar Talata, 18 ga watan Agustan 2026.

Me Oyebamiji ya ce kan zaben Osun?

Bola Oyebamiji ya ce yana mutunta matsayin hukumar zabe, tare da goyon bayan matakin jam’iyyar na sake duba sakamakon zaben.

Ya yaba wa mambobin jam’iyyar, shugabanninta, masu aikin sa-kai da masu kada kuri’a da suka marawa takararsa baya, yana mai cewa jajircewarsu da sadaukarwar da suka nuna a tsawon yakin neman zaben ba za su gushe daga zuciyarsa ba.

“Ko da yake mun yi fatan samun wani sakamako na daban a zaben, a halin yanzu muna mutunta matsayin hukumar zabe kuma ina matukar goyon bayan matakin da jam’iyyarmu ta dauka na ci gaba da sake duba sakamakon zaben.” In ji shi

Yakin neman zabe bai kare komai ba

Kara karanta wannan

APC ta saba da Tinubu kan zaben Osun, ta bayyana matsayarta kan nasarar Adeleke

Dan takarar APC ya ce kammala yakin neman zabe da zaben ba yana nufin kawo karshen dabi’u da manufofin da yakin neman zabensa ya kunsa ba.

A cewarsa, shi da magoya bayansa za su ci gaba da aiki domin ganin an samu “ci gaba mai inganci, wanda ya hada kowa da kowa kuma cikin sauri” a jihar Osun.

Ya bukaci mambobin jam’iyyar da magoya bayanta su ci gaba da kasancewa cikin harkokin siyasa, cikin tsari da jajircewa wajen aiki domin moriyar jihar baki daya.

Shawarar Oyebamiji ga magoya bayan APC

Yayin da yake kira ga magoya bayansa da su zauna lafiya, Oyebamiji ya bukace su da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da komawa ga tashin hankali ba.

Ya kuma nuna godiya ga dukkan masu kada kuri’ar da suka marawa takararsa bayaf, da kuma mambobin jam’iyya, shugabanni da masu aikin sa-kai da suka taka rawa wajen yakin neman zabensa.

Oyebamiji ya fadi zaben gwamnan Osun
Bola Oyebamiji a wajen yakin neman zabe Hoto: Bola Oyebamiji
Source: Facebook

Abin da ya sa APC ta fadi zaben Osun

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC, Farouk Aliyu, ya haska dalilin da ya sa jam'iyyar ta yi rashin nasara a zaben gwamnan Osun.

Farouk Aliyu ya bayyana rikicin cikin gida, rashin jituwa kan dan takararta da kuma raina karfin masu kada kuri’a sun taimaka wajen kayar da ita a zaben gwamnan jihar Osun na 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng