'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kan Mutane a Kwara, Rayuka Sun Salwanta

'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kan Mutane a Kwara, Rayuka Sun Salwanta

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'addanci a jIhar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Ƴan bindigan sun hallaka mutum shida a wani hari da suka kai a yankin Ilesja-Baruba inda suka buɗewa mutane wuta
  • Rundunar ƴan sandan jihar Kwara ta tabbatar da aukuwar harin, ta ƙara da cewa ta cafke wani mai ba ƴan bindiga bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kwara.

Harin da bindigan suka kai a Ilesha-Baruba da ke Arewacin jihar ya yi sanadiyyar hallaka mutum bakwai ciki har da wani ɗan sa-kai.

'Yan bindiga sun kai hari a Kwara
'Yan bindiga sun hallaka mutum 7 a Kwara Hoto: @PoliceNG (X)
Asali: Facebook

Rundunar ƴan sandan jihar Kwara ta tabbatar da aukuwar harin a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun tabbatar da harin ƴan bindiga

Rundunar ta kuma bayyana cewa an kama wani mai bai wa ƴan bindiga bayanai, yayin da aka ƙara ƙaimi wajen ɗaukar matakan tsaro a yankunan da abin ya shafa, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Mai magana da yawun rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ya ce rundunar tana bincike kan hare-haren da suka auku a ƙananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar.

"Da misalin ƙarfe 9:30 na dare, wasu ƴan bindiga kimanin mutum 10, sun afka tashar motar Ilesha–Baruba inda suka buɗe wuta kan fararen hula da ke wani wajen hutawa."
"Sakamakon haka, mutane shida da aka gano sunayensu da suka haɗa da Alhaji Ja’awire, AbdulJabar, Mohammed Nasamu da wasu uku, sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka jikkata sosai sakamakon harbin bindiga."
"An kai gawarwakin mamatan zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na Ilesha–Baruba domin yin bincike, yayin da waɗanda suka jikkata ke karɓar magani."
"An fara gudanar da bincike, kuma an ɗauki cikakken matakin tsaro domin kamo masu hannu a wannan aika-aika."

- Toun Ejire-Adeyemi

Ƴan sa-kai sun fafata da ƴan bindiga

Abdulrahman Abdulrazaq
'Yan bindiga sun kai hari a Kwara Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Asali: Facebook
“A wani lamari mai alaƙa da hakan da misalin ƙarfe 11:30 na safe, wata ƙungiyar ƴan sa kai daga Kemanji da ke gudanar da sintiri a ƙafa, ta ci karo da wasu da ake zargin ƴan bindiga ne a cikin gandun dajin Kainji."
“Yayin musayar wuta, wasu uku daga cikin ƴan bindigan sun samu raunukan harbin bindiga wanda yi sanadiyyar mutuwarsu, yayin da wani ɗan sa kai mai suna Yusuf Samba ya samu rauni kuma daga baya ya rasu."
“Bincikenmu ya kai ga kama wani mai bayar da bayanai, wanda ya amsa cewa yana aiki tare da wata ƙungiyar ƴan bindiga. Wannan mutum ya zama muhimmanci a ci gaba da binciken da ake yi."

- Toun Ejire-Adeyemi

Ƴan bindiga sun kai hari a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Kware da ke jihar Neja.

Ƴan bindiga sun hallaka mutum ɗaya tare da raunata wasu da dama a harin da suka kai a cikin tsakar dare.

Miyagun ƴan ta'addan sun kuma cinna wuta ga babbar kasuwar garin a hanyarsu ta ficewa bayan sun gama aika-aikar da za su yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng