'Yan Bindiga Sun Kai Harin Ta'addanci a Sokoto, Sun Tafka Gagarumar Barna
- Ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a garin Kware wanda nan ne hedkwatar ƙaraamar hukumar Kware a jihar Sokoto
- Miyagun sun riƙa harbi kan mai uwa da wabi bayan sun dura a garin da daren ranar Asabar, 19 ga watan Afirilun 2025
- Ƴan bindigan sun cinnawa kasuwar garin wuta yayin da suka raunata wasu mutane da ba a bayyana adadinsu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari a garin Kware da ke jihar Sokoto.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Asabar wanda ya jefa mutane cikin firgici.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce shaidu sun bayyana cewa mahara masu yawa ne suka shigo cikin garin wanda nan ne hedkwatar ƙaramar hukumar Kware.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun kai hari a Sokoto
Ƴan bindigan sun riƙa harbi kan mai uwa da wabi domin tarwatsa ƴan kasuwa da masu siyayya kafin su banka wa Kasuwar Kware wadda ake ji da ita wuta.
An tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, yayin da wasu da dama suka samu raunuka, kuma a halin yanzu suna samun kulawar likita a wani asibitin da ke cikin birnin Sokoto.
A cewar wani ganau kuma mazaunin garin, Malam Zaharadeen Kware, maharan sun yi nufin kai hari ne kan wani shahararren ɗan kasuwa, wanda aka ɓoye sunansa.
Sai dai, kafin ƴan bindigan su iso garin, ɗan kasuwa ya rufe shagon nasa bayan ya tashi daga kasuwar.
Ƴan bindigar ba su tsaya nan ba, sun banka wa shagon nasa wuta tare da cinna wuta a kasuwar garin.
Garin Kware, wanda ke kan hanyar Sokoto zuwa Illela, ya daɗe yana fama da matsalar tsaro, kuma ana zargin akwai masu ba da bayani ga ƴan ta’adda a cikinsa.
Wannan zargi ya ƙara ƙarfi sakamakon yadda aka kai harin na baya-bayan nan cikin ƙwarewa.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Asali: Twitter
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce ƴan bindigan sun harbi mutum biyu, amma daga baya guda ɗaya ya rasu yayin da aka garzaya da ɗayan zuwa asibiti.
"A hanyar ƴan bindigan ta barin garin, sun cinnawa dajin da ke bayan gari wuta wadda ta shafi kasuwar garin."
"Sun harbi mutum biyu inda suka bar su da raunin bindiga, abi takaici ɗaya ya rasu yayin da aka garzaya da ɗayan zuwa asibiti."
- Kakakin ƴan sandan Sokoto
Ƴan bindiga sun kai.hari a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a garin Faruruwa da ke ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano.
Mummunan harin da ƴan bindigan suka kai ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum biyu yayin da suka kuma yi awon gaba da wasu mutum biyu.
Shugaban ƙaramar hukumar Shanono wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya yi tir da ta'addancin da ƴan bindigan suka yi.
Asali: Legit.ng