Yaki da 'Yan Bindiga: Yadda Gwamnatin Katsina Ta Kashe N36bn kan Samar da Tsaro

Yaki da 'Yan Bindiga: Yadda Gwamnatin Katsina Ta Kashe N36bn kan Samar da Tsaro

  • Gwamnatin jihar Katsina ta yi bayani kan maƙudan biliyoyin da ta kashe wajen yin fito na fito da matsalar rashin tsaro
  • Mataimakin gwamnan Katsina, ya bayyana cewa ayyukan samar da tsaro a jihar sun laƙume maƙudan kuɗi har N36.8bn
  • Faruk Lawal Jobe ya bayyana cewa an kashe dukiyar wajen samar da rundunar tsaro, sayo kayan aiki da sauransu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina tare da ƙananan hukumominta 34 sun kashe Naira biliyan 36.8 domin tunkarar matsalar rashin tsaro a faɗin jihar.

Mataimakin gwamnan Jihar, Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a Katsina.

Gwamna Dikko Radda
Gwamnatin Katsina ta kashe N36.8bn kan samar da tsaro Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Ya ce adadin kuɗin an kashe su ne tun daga lokacin da wannan gwamnati ta hau mulki zuwa yanzu, cewar rahoton jaridar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe N36bn kan tsaro a Katsina

Ya bayyana cewa an kashe kuɗin wajen sayan motocin yaƙi masu sulke guda 10, motocin Toyota Hilux guda 65 da kuma babura nau’in Daylong guda 700.

"Sayan kayan yaƙi na musamman guda 1,900 don fara aikin rundunar C-Watch, wadda gwamnati ta ƙirƙiro don tabbatar da tsaro a cikin al’umma."
"Biyan alawus na kowane wata ga mambobin ƴan sa-kai 1,500, ƙungiyoyin tallafi na al’umma 1,279, shugabannin unguwanni 6,652, limamai 2,515, masu kiran salla 2,515 da mataimakan limamai 2,515."
"Ɗaukar ma’aikata, bayar da kayan aiki da horo ga rukuni na farko da na biyu na jami’an rundunar C-Watch."
"Ba da horo ga masu aikin sa-kai 1,100 daga ƙananan hukumomi takwas da ke fama da barazanar ƴan bindiga."

- Faruk Lawal-Jobe

Gwamnatin Katsina ta tallafawa jama'a

Faruk Lawal Jobe ya ƙara da cewa gwamnati ta kashe Naira miliyan 985.9 kan kuɗaɗen magunguna, taimakon kuɗi da sauran nau’ikan taimako ga waɗanda suka fuskanci hare-haren ƴan bindiga.

Faruk Lawal Jobe
Gwamnatin Katsina ta kashe kudade kan rashin tsaro Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Jobe ya bayyana cewa mutane 2,286 ne suka amfana da wannan tallafi zuwa yanzu.

Ya kuma ce an ɗauki jami’an rundunar C-Watch 1,466 a mataki na farko kuma an tura su zuwa ƙananan hukumomi takwas da ke sahun gaba wajen fama da matsalar tsaro.

Waɗannan kananan hukumomi sun haɗa da, Dandume, Faskari, Kankara, Danmusa, Batsari, Jibia, Sabuwa da Safana.

A mataki na biyu kuwa, an tura jami’ai 550 zuwa ƙananan hukumomi 10 masu fuskantar barazana, Bakori, Musawa, Malumfashi, Danja, Funtua, Matazu, Charanchi, Batagarawa, Kurfi da Dutsin-Ma.

Mataimakin gwamnan ya ƙara da cewa an ɗauki mafarauta guda 200 domin ƙara ƙarfafa aikin jami’an tsaro.

Jami'an tsaro sun yi galaba kan ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'am tsaro sun samu nasarar daƙile wasu hare-haren da ƴan bindiga suka kai a jihar Katsina.

Jami'an tsaron sun daƙile hare-haren ne a wasu yankunan ƙaramar hukumar Malumfashi da ke jihar.

Nasarar da jami'an tsaron suka samu ta biyo bayan musayar wutar da suka yi da ƴan bindigan masu ɗauke da makamai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng