Lokaci Ya Yi: Hadimar Gwamna Sheriff Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, An Fara Zargin Mijinta

Lokaci Ya Yi: Hadimar Gwamna Sheriff Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, An Fara Zargin Mijinta

  • Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya rasa ɗaya daga cikin hadimansa mata yau Litinin, 21 ga watan Afrilu, 2025
  • Mai ba gwamnan shawara kan harkokin kasuwanci da safara ta riga mu gidan gaskiya bayan fama da ƴar gajeruwar jinya
  • Rundunar ƴan sanda sun ce ana tsare da mijinta domin ba shi kariya saboda ƴan uwanta na zarginsa da hannu a mutuwarta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Mai ba gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, Love Shimite, shawara ta musammman kan harkokin kasuwanci da safara zuwa waje, ta riga mu gidan gaskiya.

Hadimar gwamnan ta mutu ne yau Litinin, 21 ga watan Afrilu, 2025 ranar da mabiya addinin kirista ke bikin ista na bana.

Cif Love Shimite.
Hadimar gwamnan jihar Delta, Love Shimite ta Rasu a ranar bikin ista Hoto: Ossai Ovie Succes
Asali: Facebook

Hadimar Gwamna Sheriff ta rasu

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna majiyoyi sun bayyana cewa ta rasu ne sakamakon wata gajeriyar rashin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai har kawo yanzu ba a tantance cikakken abin da ya haddasa mutuwarta ba, lamarin da ya ɗaga hankalin ƴan uwanta.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Delta, Mr. Bright Edafe, ya tabbatar da rasuwar Love Shimite a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin

Ya bayyana cewa marigayiya Shimite ta rasu ne a asibiti bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Ƴan sanda sun yi magana kan rasuwar

Kakakin ƴan sandan ya kara da cewa mijinta ya kira ofishin ‘yan sanda domin sanar da rasuwar da kuma cewa yana fuskantar barazana daga ‘yan uwan matarsa.

Edafe ya ce:

“Mijinta ne ya kira mu ya sanar cewa matarsa ta mutu tun safe, kuma ya fara samun barazana daga ‘yan uwanta, ya ce ya na zargin za su iya farmakarsa.
"Saboda haka ne muka je gidansa muka dauko shi don kare lafiyarsa, ba don kama shi ba. Yanzu dai muna tsare da shi."

Love Shimite.
Yan sanda sun fara bincike kan rasuwar hadimar gwamnan Delta Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

An fara zargin mijin hadimar gwamna

Sai dai daga bisani, iyalan marigayiyar sun kai korafi ofishin ‘yan sanda, sun bayyana cewa suna zargin cewa mijinta na da hannu a rasuwarta.

Edafe ya kara da cewa:

“Yanzu haka muna gudanar da bincike. A irin wannan lamari, gwajin gawa ne zai tabbatar ko mutuwar ta kasance ta dabi’a ce ko kuma akwai wani dalili daban.”

‘Yan sanda sun tabbatar cewa sun fara bincike tare da alkawarin sanar da jama’a da zarar an samu ci gaba, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Hadiman gwamnan Kano ya kwanta dama

A wani rahoton, kun ji cewa jihar Kano ta shiga jimami da Allah ya yi wa mai taimaka Gwamna Abba Kabir Yusuf kan harkokin matasa, Abdullahi Salisu Furfura rasuwa.

An ruwaito cewa marigayin ya riga mu gidan gaskiya ne sa'o'i ƙalilan bayan ya wallafa sako a shafinsa na dandalin sada zumunta watau Facebook.

Rahoton ya tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana'izar marigayin a ranar Juma'a 18 ga watan Afrilun 2025 da misalin karfe 10:00 na safe a unguwar Giginyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262