An Shiga Jimami bayan Wani Abin Fashewa Ya Fashe a Kaduna, an Samu Asarar Rayuka
- Fashewar wani abin fashewa ta jawo an samu asarar rayukan mutane a jihar Kaduna da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Lamarin wanda ya auku a ranar Talata, 22 ga watan Afirilun 2025 ya jawo rasuwar wasu yara guda biyu, ɗaya mai shekara 13, sai ɗayar mai shekara shida
- Hakazalika fashewar wacce ba a san musabbabinta ba, ta jawo wasu mutane uku kuma sun samu raunuka
- Wani mazaunin yankin da lamarin ya auku, ya bayyana cewa yana cikin gida yana wanka ya jiyo ƙarar fashewar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - An samu asarar rayuka bayan wani abin fashewa ya fashe a jihar Kaduna.
Yara biyu, wani yaro mai shekaru 13 mai suna Imam da wata yarinya ƴar shekara shida mai suna Nasrin, sun mutu sakamakon fashewar.

Asali: Original
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a unguwar Abakpa da ke jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin fashewa ya tarwatse a Kaduna
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mazauna yankin guda uku sun samu raunuka a sanadiyyar fashewar, wacce ta faru a ranar Talata, 22 ga watan Afirilun 2025.
Lamarin ya auku ne a kusa da tsohon wurin da makarantar horar da sojoji ta Najeriya Kaduna take.
Har yanzu ba a tantance musabbabin fashewar ba, amma hukumomin tsaro na nan a wurin don gudanar da bincike kan lamarin.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa yana cikin yin wanka ne lokacin da ya ji ƙarar fashewar, inda nan da nan ya fito da sauri.
“Fashewar ta faru ne kusa da gidana sosai. Da na ji ƙarar, sai na fito don ganin abin da ya faru. Na ga ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, wato Imam, sai na yi ƙoƙarin kai shi asibiti, amma ya rasu kafin mu isa.”
- Wata majiya
Har ya zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai game da musabbabin fashewar ba, amma lamarin ya jefa al’umma cikin tsoro da tashin hankali, domin har yanzu mazauna yankin na cikin firgici.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Asali: Twitter
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta musanta cewa fashewar bam ya auku a unguwar Abakpa, cewar rahoton tashar Channels tv.
Mai magana da yawun rundunar, Mansir Hassan, ya bayyana cewa binciken farko da sashen masu kula da bam ya gudanar ya nuna cewa wata bindigar maharba ce da aka harba ta janyo lamarin.
Ya ƙara da cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar Talata, a kan titin Josawa da ke unguwar Abakpa, inda wani yaro mai shekaru 12 ya rasa ransa, yayin da wasu mutum bakwai suka samu raunuka daban-daban.
Abin fashewa ya tarwatse da ƴan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani abin fashewa ya tarwatse da wasu jami'an ƴan sanda a jihar Borno.
Lamarin wanda ya auku a kan titin Maiduguri/Damaturu ya janyo sanadiyyar jikkata jami'an ƴan sanda mutum uku.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP ake zargi da dasa nakiyar wacce ta tarwatse da jami'an ƴan sandan a kan hanyar.
Asali: Legit.ng