Yadda Jami'an NDLEA Suka Cafke Hodar Iblis da Za a Kai Saudiyya cikin Littattafan Addini
- Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) sun samu nasarar hana yin safarar wata hodar iblis zuwa ƙasar Saudiyya
- An cafke hodar iblis ɗin ne bayan an ɓoye ta a cikin wasu littatafan addini a wani kamfanin jigilar kayayyaki da ke jihar Legas
- Hazalika, jami'an na hukumar NDLEA sun cafƙe wani matashi mai safarar miyagun ƙwayoyi ga ƴan bindiga a jihar Katsina
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jami’an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) sun kama wani ƙunshin hodar iblis da za a kai Saudiyya.
Jami'an na NDLEA sun gano hodar iblis ɗin ne wacce aka ɓoye a cikin littattafan addini guda 20 da ake shirin tura wa ƙasar Saudiyya.

Asali: Twitter
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cafke hodar iblis da za a kai Saudiyya
A cewar sa, an gano hodar iblis ɗin ne a wani kamfanin jigilar kaya da ke Legas a ranar Talata, 15 ga watan Afrilu, 2025, lokacin da jami’an sashin ayyuka da bincike na NDLEA (DOGI) ke bincikar kayayyakin fitarwa zuwa Saudiyya.
Hodar iblis ɗin wadda ta ƙunshi ƙulli guda 20 na da nauyin gram 500, kuma an ɓoye su ne a cikin shafukan littattafan addinin domin yin basaja.
A jihar Kano kuwa, jami’an NDLEA sun cafke wani matashi mai shekaru 22 mai suna Muhammad Mohammed, wanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi ga ƴan ta’adda.
An kama shi ne a lokacin da yake tafiya zuwa jihar Katsina a kan hanyar Bichi zuwa Kano ɗauke da allurai 277 na pentazocine da ya ɗaure da silataf a cinyarsa da gabansa.
An kama Muhammad ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Afrilun 2025.
Jami'an NDLEA sun cafke masu laifi

Asali: Twitter
"Haka zalika, a wannan rana, an kama wani da ake zargi mai suna Mohammed Abdulrahman Abdulaziz mai shekaru 43 a unguwar Research Rimin Kebe da ke ƙaramar hukumar Nasarawa, Kano. An kama shi da ƙulli 68 na tabar wiwi masu nauyin kilogram 30."
"Baya ga haka, an ƙwato fiye da kilogram 557.2 na wiwi, kilogram 5.6 na methamphetamine da gram 29.8 na ƙwaya daga wani gida da ke kan titin Major General Isaiah Allison, Opolo, Yenagoa, jihar Bayelsa."
"Jami’an NDLEA sun kai samamen ne a gidan ne a ranar Laraba, 16 ga watan Afrilun 2025."
"Mutane huɗu da ake zargi sun shiga hannun jami’an NDLEA a lokacin samamen, waɗanda suka haɗa da, Sarimiye Suwa Kurtis, mai shekaru 46, Roland Prosper, mai shekaru 34, Sarimiye Tare Paul, mai shekaru 45 da Fidelis Ugbesla, mai shekaru 46."
- Femi Babafemi
Jami'an NDLEA sun cafke tsoho a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar NDLEA sun samu nasarar cafke wani tsoho mai shekara 75 da ke safarar miyagun ƙwayoyi a Kano.
Jami'an na hukumar NDLEA sun cafke tsohon ne a ƙauyen Tumbau da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano.
Dattijon mai suna Nuhu Baba, ya bayyana cewa ya kwashe shekara biyu yana muguwar sana'ar domin samun na abinci.
Asali: Legit.ng