"Gwamnati Ta Yi Kadan": Tsohon Ministan Tsaro Ya ba 'Yan Najeriya Mafita kan 'Yan Bindiga

"Gwamnati Ta Yi Kadan": Tsohon Ministan Tsaro Ya ba 'Yan Najeriya Mafita kan 'Yan Bindiga

  • Tsohon ministan tsaro, Janar T. Y. Danjuma (mai ritaya) ya koka kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a ƙasar nan
  • Janar Thiophilus Yakubu Danjuma ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta fi ƙarfin gwamnati ita kaɗai ta magance ta
  • Dattijon na ƙasa ya yi kira ga ƴan Najeriya da su tashi tsaye su kare kansu daga hare-haren ƴan bindiga da kuma ƴan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Tsohon ministan tsaro, Janar T. Y. Danjuma (mai ritaya), ya yi magana kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a ƙasar nan.

Janar T. Y. Danjuma ya jaddada cewa yaƙi da rashin tsaro a Najeriya ba abu ba ne da za a bar wa gwamnati ita kaɗai.

T. Y Danjuma ya shawarci 'yan Najeriya su kare kansu
Janar T. Y. Danjuma ya shawarci 'yan Najeriya kan su kare kansu Hoto: TY Danjuma Foundation
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce ya yi wannan kira ne a lokacin wani taron girmamawa da aka shiryawa ma’aikatansa a Takum, jihar Taraba, a ƙarshen mako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara T. Y. Danjuma ya ba da?

Ya shawarci ma’aikata, abokan aiki, da kamfanonin da ke aiki tare da shi da ka da su zauna hannu biyu suna kallon yadda ƴan bindiga da ƴan ta’adda ke mamaye ƙauyuka da garuruwansu.

Dattijon ya yi gargaɗin cewa idan ƴan ƙasa ba su tashi tsaye ba don kare kansu, to ƴan ta’adda da ƴan bindiga za su ci gaba da mamaye garuruwa, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Ya jaddada muhimmancin shiri don kare kai, yana mai cewa hakan wajibi ne duba da yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a faɗin ƙasar nan.

A cewarsa, yawaitar kashe-kashen da ake samu a jihohin Benue, Plateau da wasu sassan ƙasar nan, sun sake tabbatar da kiran da ya yi tun da daɗewa na mutane su tashi su kare kansu.

"Mun fuskanci matsalar garkuwa da mutane, kuma barazanar hakan na ci gaba. Wannan bala’i ba zai tsaya ba har sai mu, kowane ɗayanmu, mun tashi tsaye domin kare kanmu."

“Gargaɗin da na yi shekarun da suka gabata har yanzu yana da muhimmanci kamar yadda yake a wancan lokacin. Dole ne ƴan Najeriya su tashi tsaye su kare kansu."
“Ba za mu ci gaba da zama mu na kallo ba yayin da ƴan bindiga, ƴan ta’adda da ke ci gaba da kashe mutane ba tare da an ɗauki mataki ba."
"Yanzu ya bayyana a fili cewa gwamnati ita kaɗai ba za ta iya kare mu ba. Dole ne mu tashi tsaye mu kare kanmu, iyalanmu, da ƙasarmu kafin waɗannan miyagun mutane su mamaye ƙasar gaba ɗaya."

- Janar T. Y. Danjuma

Tsohon ministan tsaro ya godewa ma'aikatansa

Janar T. Y. Danjuma
Janar T. Y. Danjuna ya yaba da kokarin ma'aikatansa Hoto: TY Danjuma Foundation
Asali: UGC

Janar Danjuma ya nuna godiya ƙwarai ga ma’aikatansa da abokan aikinsa saboda sadaukarwarsu da ƙwazon da suka nuna, musamman waɗanda ke aiki a cibiyar lafiya ta TY Danjuma.

Ya yaba da irin hidimar da suke yi da kuma yadda suke ba da gudunmawa wajen gina suna mai kyau ga cibiyar, yana mai cewa bai manta da ƙoƙarinsu ba.

Ƴan bindiga sun kai hari a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a garin Kware da ke jihar Sokoto.

Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutum ɗaya tare da raunata wasu da dama waɗanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Ƴan bindigan sun kuma cinnawa babbar kasuwar garin wuta a yayin harin wanda suka kai da daddare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng