Jigo a SDP Ya Aika da Sabon Gargadi ga El Rufai kan Shugaba Tinubu
- Adewole Adebayo wanda ya nemi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya ja kunnen tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai
- Adebayo ya bayyana cewa ba za su bari wasu da ke fushi da Shugaba Bola Tinubu su karɓe jam'iyyar SDP domin yin yaƙi da shi ba
- Ya bayyana cewa jam'iyyar SDP ba wuri ba ne da za a tsaya a riƙa ƙulla makirci irin na siyasa don cimma wata manufa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP a zaɓen 2023, Prince Adewole Adebayo, ya yi gargaɗi ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Adewole Adebayo ya ce El-Rufai da sauran shugabannin adawa ba za su iya karɓe jam’iyyar SDP ba domin amfani da ita wajen yaƙi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana haka ne a wajen bikin cika shekaru 50 da haihuwa na matarsa, Queen Lillian Adebayo, da aka gudanar da daren ranar Litinin a birnin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane gargaɗi 'dan takaran SDP ya yi?
Adewole Adebayo ya ce jam’iyyar SDP ba waje ba ne da za a riƙa haɗa makirci ba, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
El-Rufai dai ya kasance abin magana bayan ficewarsa daga APC mai mulki, wadda ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ta.
Sai dai Adebayo, wanda ya bayyana cewa har yanzu yana cikin masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, ya jaddada cewa jam’iyyar SDP ba dandali ba ce don rikicin siyasa na ƙashin kai.
“Tabbas, jam’iyyata ta san cewa ni ɗan takara ne a zaɓen 2027. Game da haɗaka, muna sauraren su. Ba mu shirya zama mota ta tsere domin makirci da sata da ba mu da hannu a ciki ba. Wannan ba zai yiwu ba."
“Idan haɗakar don al’umma ce, SDP a shirye take. Amma idan an yi ta ne kawai don mutanen da Tinubu ya fusata, su koma wurinsa su warware matsalolinsu a can. Ka da su zo SDP su nemi yin amfani da mu wajen faɗan da ba mu da hannu a ciki."
Dangane da kashe-kashen da ake yi a jihar Benue, Plateau da wasu sassan ƙasar nan, Adebayo ya buƙaci shugaban ƙasa da ya sake tsara dabarun tsaro don magance matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar.

Asali: Facebook
An caccaki shirin haɗakar Atiku & El-Rufai
Hakazalika a wajen taron, tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi watsi da yunƙurin haɗaka wasu ƴan adawa ke yi a yanzu gabanin zaɓen 2027.
Omoyele Sowore ya ce yana goyon bayan haɗaka da adawa a tsarin dimokuradiyya, amma ya bayyana cewa mutanen da ke jagorantar wannan yunkuri yanzu ba su da gaskiyar da za su iya kawo sahihin sauyi.
Nasir El-Rufai ya caccaki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai, ya caccaki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
El-Rufai ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya taɓarɓarar da komai a ƙasar nan fiye da lokacin da ya ƙarɓi mulki.
Tsohon ministan ya bayyana cewa tsaro ya taɓarɓare sannan masu hali arziƙinsu ya yi baya a mulkin Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng