Zaben 2027: Gatan da APC Ke Shirin Yi Wa Shugaba Bola Tinubu

Zaben 2027: Gatan da APC Ke Shirin Yi Wa Shugaba Bola Tinubu

  • Jam'iyyar APC na shirin yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu gata idan ya nemi ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027
  • Alamu sun nuna cewa APC na iya ba Tinubu tikitin takarar shugaban ƙasa ba tare da hamayya ba a zaɓen 2027 da ke tafe nan gaba
  • Majiyoyi daga hedkwatar APC a Abuja sun bayyana cewa kwamitocin NWC da NEC ke da alhakin zartar da irin wannan hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Alamu na nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki, na iya bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu tikitin takara ba tare da hamayya ba domin yin tazarce a 2027.

Hakan na zuwa ne yayin da ƴan adawa ke ƙoƙarin yin haɗaka domin tunkarar shi a babban zaɓen shekarar 2027.

Bola Tinubu
Tinubu na iya samun tikitin tazarce ba tare da hamayya ba Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Majiyoyi daga hedikwatar APC da ke Abuja sun tabbatar da yiwuwar wannan mataki a tattaunawar da jaridar The Punch ta yi da su daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai samu tikitin APC a 2027?

Wasu daga cikin waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu sun jaddada cewa, la’akari da kasancewa mai riƙe da madafun iko, shugaban ƙasan zai samu haƙƙin farko na ƙin yarda da neman tazarce.

Mataimakin shugaban APC na ƙasa yankin Kudu maso Gabas, Dr. Ijeoma Arodiogbu, ya bayyana cewa bai wa shugaban ƙasa tikitin kai tsaye ba abu ne da ba a saba yi ba.

Sai dai Arodiogbu ya bayyana cewa irin wannan hukunci sai dai idan kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) da kuma kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) sun amince da shi.

“Ina ganin wannan hukunci ne da zai dogara da abin da NWC da NEC suka yanke. A zaman da NEC ta yi na baya-bayan nan, mun amince da Tinubu a matsayin wanda jam’iyya ke goyon baya don tazarce. Wannan daidai yake da ba shi tikitin kai tsaye."

- Dr. Ijeoma Arodiogbu

Ya kuma ce ba zai yiwu a cire yiwuwar siyar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa ga wasu masu sha’awa ba, idan NEC ta yanke shawarar sauya matsayinta daga goyon bayan da ta bayar.

APC za ta ba masu son yin takara dama

Bola Ahmed Tinubu
Har yanzu Bola Tinubu bai ce zai sake tsayawa takara ba Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Mataimakin sakataren tsare-tsaren jam’iyyar na ƙasa, Nze Chidi Duru, ya bayyana ra’ayi makamancin haka, inda ya jaddada cewa jam’iyyar ba za ta hana wasu masu sha’awa yin takara da Tinubu ba.

“Abu ne a bayyane cewa kowa yana da damar ƙalubalantar shugaban ƙasa. Amma bisa tsarin siyasa, na yi imani cewa shugaba mai ci wanda ke wa’adin farko, ya kamata a ba shi haƙƙin farko na yanke shawarar tsayawa ko a’a domin yin wa’adi na biyu."
“Wannan tsari ne da ke ƙarfafa ɗabi’ar yin aiki na nagari kuma yana ƙarfafa jam’iyyun siyasa su tabbatar cewa ƴaƴansu sun yi abin da ya dace."

- Nze Chidi Duru

Gwamna Sule ya magantu kan zaɓen Tinubu a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa yankin Arewacin Najeriya zai goyi bayan Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Gwamna Sule ya bayyana cewa yankin zai mutunta alƙawarin da ya ɗauka na ganin ɗan Kudu ya mulki ƙasar nan har na shekara takwas.

Ya soki wasu ƴan siyasar Arewa kan yadda suke yunƙurin kawo ruɗani domin cimma wasu manufofo na ƙashin kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng