IGP Ya Fusata, Ya Janye Ƴan Sandan Mopol daga Tsaron Manyan Mutane a Najeriya

IGP Ya Fusata, Ya Janye Ƴan Sandan Mopol daga Tsaron Manyan Mutane a Najeriya

  • Sufeta Janar, Kayode Egbetokun ya soki kwamandojin Mopol bisa yadda suke tura jami’ai wuraren da ba su da alaka da manufar aikinsu
  • Shugaban 'yan sandan ya haramta tura jami'an Mopol zuwa tsaron manyan mutane, yana mai cewa hakan ya sabawa dalilin kafa rundunar
  • IGP Egbetokun ya ce duk za a samar da tawagogin Mopol, a ba su kayan aiki, domin su kasance cikin shirin ko ta kwana daga jihohi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya yi kaca-kaca da kwamandojin rundunar ‘yan sandan MOPOL a ranar Talata.

An ce IGP Kayode Egbetokun ya fusata ne bisa yadda kwamandojin Mopol ke tura jami’an sashen zuwa tsaron manyan mutane a kasar.

Sufeta Janar na 'yan sanda ya ba da umarnin janye dukkanin jami'an Mopol da ke tsaron manyan mutane
IGP Kayode Egbetokun a ganawarsa da kwamandojin rundunar Mopol a Abuja. hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Sufeta Janar ya gana da kwamandojin Mopol

Shugaban 'yan sandan ya ba da umarni cewa daga yanzu ba za a sake tura jami’an MOPOL don kare manyan mutane (VIPs) ba, kamar yadda aka sanar a shafin rundunar na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IGP Kayode Egbetokun ya bayyana haka ne a hedikwatar rundunar da ke Abuja yayin wata ganawar gaggawa da ya yi da kwamandojin Mopol.

An ce ganawar ta biyo bayan bayan cece-kucen da ya barke kan wani faifan bidiyo da ya nuna wani dan kasar China yana ba jami’an Mopol kyautar kudi a bainar jama’a.

Tun da fari, rundunar ta gayyaci jami’an da aka gani a bidiyon domin amsa tambayoyi, sannan an ce an ɗauki matakin ladabtarwa a kansu.

"Mopol sun sauka daga aikinsu na asali" - IGP

Kafin su shiga ganawar ta ranar Talata, IGP Egbetokun ya ce ya gayyaci kwamandojin ne domin tunatar da su manufar kafa 'MOPOL', yana mai cewa ba za a yarda su sauka daga turbar da aka gina su a kai ba.

“A takaice, an sauka daga manufar da aka kafa rundunar PMF. Yanzu haka, yawancin jami’anta suna aiki ne a matsayin 'yan rakiya, masu gadi ko masu taimakawa wasu tsirarun mutane.

“Ko da yake mun fahimci dalilan da ke haddasa hakan, amma dole mu karkata kan ayyukan rundunar na asali. Tura jami’ai zuwa ayyukan da ba su dace ba, yana rage ƙarfinmu a inda ake buƙatarmu matuƙa."

- IGP Kayode Egbetokun.

Sufeta Janar ya koka cewa duk kokarin da yake yi na sake fasalin rundunar, na samun koma baya saboda rashin ƙwarewar wasu jami’an ‘yan sanda.

IGP Egbetokun ya ba da umarnin janye jami'an Mopol daga tsaron manyan mutane
Shugaban 'yan sanda, Egbetokun yayin da yake ganawa da kwamandojin Mopol a Abuja. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

IGP ya janye Mopol daga tsaron manya (VIPs)

Ya bayyana cewa ya riga ya bayar da umarni a janye dukkan jami’an MOPOL da ke tsaron manyan mutane, yana mai cewa dole a tabbatar da bin wannan doka.

“Abin damuwa mafi girma shi ne yadda wasu ke ci gaba da aikata rashin da’a duk da kokarinmu na ganin sun yi aiki da kwarewa.
“Daga yau, dukkan rukunan PMF za su kasance karkashin wata tawaga da ke da kayan aiki kuma da ke a shirye don jiran ko ta kwana daga jihohi.

“Ku sani, an bayar da umarnin janye jami’an da aka tura wuraren da ba su dace ba. Dole kwamandoji su tabbatar da wannan umarni cikin gaggawa."

- IGP Egbetokun.

Karanta sanarwar a nan kasa:

An janye 'yan sandan tsofaffin gwamnoni

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta janye jami’an tsaro na musamman da ke ba da tsaro ga wasu fitattun mutane a Najeriya, ciki har da tsofaffin gwamnoni.

Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya bada umarnin janye masu gadin tsohon sakataren gwamnatin tarayya da tsofaffin ministoci.

Umarnin ya kuma shafi tsofaffin 'yan majalisar tarayya, matar tsohon shugaban kasa Aisha Buhari da kuma wani daga cikin ‘yan uwanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.