Muhimman Abubuwan da Suka Faru kan Batun Sauya Shekar Kwankwaso zuwa APC

Muhimman Abubuwan da Suka Faru kan Batun Sauya Shekar Kwankwaso zuwa APC

Jihar Kano - Maganganu sun yi ta yawo kan batun cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso zai koma jam'iyyar APC mai mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Masu maganganun dai su na cewa tsohon gwamnan na Kano zai fice daga jam'iyyarsa ta NNPP wacce ya yi takarar shugaban ƙasa a cikinta a zaɓen 2023.

Rabiu Musa Kwankwaso
Ana ta batun cewa Kwankwaso zai koma APC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Kwankwaso bai ce komai ba kan komawa APC

Sai dai, Kwankwaso bai fito ya ce wani abu ba kan raɗe-raɗin cewa zai koma tsohuwar jam'iyyarsa ta APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma dai makusantansa da manyan jiga-jiga a cikin jam'iyyar NNPP sun fito sun musanta wannan jita-jitar da ake yaɗawa.

Ga wasu muhimman abubuwa da suka faru kan batun komawar Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC:

1. Ganduje ya ce Kwankwaso zai koma APC

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa jam'iyyar NNPP shaguɓe ta hanyar cewa ta mutu murus, cewar rahoton jaridar The Punch.

Ganduje ya kuma bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara yunƙurin tattara kayansa zuwa APC.

Shugaban na APC ya ce Kwankwaso ya fara yunƙurin komawa APC ne domin ya fahimci cewa ya rasa komai a jam'iyyar NNPP.

Ganduje ya bayyana cewa ƙofa a buɗe take ga Kwankwaso domin ya dawo APC, kuma za su yi masa tarba ta musamman.

2. APC ba ta maraba da Kwankwaso a Kano

Mai magana da yawun jam'iyyar APC a jihar Kano, Ahmed S. Aruwa ya bayyyana cewa ba su maraba da Rabiu Musa Kwankwaso zuwa cikin APC.

A wata tattaunawa da Legit Hausa, Ahmed S Aruwa ya bayyana cewa Kwankwaso yana da halin tursasa ra'ayinsa a duk inda yaje.

Ya kuma zargi tsohon gwamnan na jihar Kano da yin kalamai marasa daɗi ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ahmed S. Aruwa ya ƙara da cewa Kwankwaso ya fara tunanin komawa APC ne bayan ya hango kuraye a cikin tafiyar haɗakar jam'iyyun adawa.

3. Buba Galadima: 'Kwankwaso ba zai koma APC ba'

Babban jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi watsi da batun cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, zai koma APC mai mulki.

A cewar rahoton jaridar The Guardian, Buba Galadima ya bayyana cewa babu wani mutumin da ya san abin da yake yi, da zai koma APC a ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje.

Buba Galadima ya bayyana cewa da ba domin ikon Shugaba Bola Tinubu ba, babu yadda za a yi Ganduje ya zama shugaban jam'iyyar APC.

4. NNPP ta magantu kan ficewar Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwaso
NNPP ta ce Kwankwaso ba zai koma APC ba Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta musanta batun cewa jagoranta na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso zai fice daga jam'iyyar.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa mai magana da yawun jam'iyyar NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, ya ƙaryata zargin cewa Kwankwaso zai koma APC.

Ladipo Johnson ya bayyana cewa furucin da Abdullahi Umar Ganduje ya yi ba shi da wani tasiri, kuma ya yi su ne tsoron da yake da shi kan tasirin da Kwankwaso yake da shi a siyasance.

Mai magana da yawun na NNPP ya ƙara da cewa Kwankwaso na ƙoƙarin farfaɗo da jam'iyyar domin fuskantar babban zaɓen shekarar 2027.

5. APC ta gindaya sharaɗi ga Kwankwaso

Jam'iyyar APC a jihar Kano ta bayyana cewa tana son duk mai son shigowa cikinta ciki har da Rabiu Musa Kwankwaso da su nemi afuwa daga shugabanni.

Jaridar The Nation ta ce shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa suna maraba da duk mai son shigowa cikinta, amma sai sun cika sharuɗɗan da aka gindaya.

Aɓdullahi Abbas ya ƙara da cewa APC ce kawai mafita ga Rabiu Musa Kwankwaso domin bai da sauran wata dangantaka mai kyau da sauran gidajen siyasar da ke ƙasar nan.

Kwankwaso ya ba gwamnati shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna takaicinsa kan rikicin da ke faruwa a jihar Plateau.

Kwankwaso ya shawarci hukumomi da su gaggauta ɗaukar matakin kamawa tare da hukunta masu hannu a kashe-kashen da ake yi a jihar.

Tsohon gwamnan na jihar Kano, ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye haiƙan wajen ganin cewa ta kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng