2027: Jigo a PDP Ya Manta da Bambancin Jam'iyya, Ya ba Peter Obi Shawara
- Babban kusa a jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi ya taɓo batun zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da ake tunkara
- Sowunmi ya shawarci Peter Obi na jam'iyyar LP da ya sauya sheƙa zuwa PDP kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Jigon na PDP ya bayyana cewa Peter Obi zai ba da mamaki idan ya yi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya ba Peter Obi shawara kan zaɓen 2027.
Segun Sowunmi ya ce ya kamata Peter Obi ya bar LP domin ya koma jam’iyyar PDP kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Asali: Facebook
Segun Sowunmi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a cikin shirin Mic On podcast da Seun Okinbaloye ke shiryawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara jigon PDP ya ba Peter Obi?
Jigon na PDP ya bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar LP yana buƙatar dandalin siyasa mai ƙarfi.
"Yayin da muka tunkari 2027, jam'iyyar PDP za ta fara shirye-shirye, ta sanar da lokacin fitar da fom ɗin takara, kuma duk wanda ke da ƙwarin guiwa ya fito ya tsaya takara."
"Idan da ni ne Peter Obi, da na dawo PDP domin na nemi tikitin takarar shugaban ƙasa. Ina ganin ya kamata ya dawo jam’iyyar."
“Wannan jam’iyyar an fara ƙirƙirarta ne a ɗakin Alex Ekwueme, don haka ban ga dalilin da ya sa mutanen Igbo da sauran shugabannin Kudanci da manyan jiga-jigai a PDP ba za su iya haɗuwa su ce, ‘To shikenan, mun yarda ga tikitin nan.’"
“Idan Peter Obi ya iya samun sama da ƙuri’u miliyan shida shi kaɗai, ba tare da goyon bayan gwamnoni ko manyan jiga-jigai ba, ka yi tunanin abin da zai iya cimmawa idan yana da gwamnoni 12."
"Muna da wakilci a duk yankuna, sai dai har yanzu ba mu kai Kudu maso Gabas ba. Amma dai Peter Obi yana da ƴancin yanke hukuncin da ya ga dama."

Asali: Facebook
“Idan alƙaluman da ke tare da shi da kuma masu goyon bayansa suka shigo PDP tare da shi kuma ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa, zan iya tabbatar maka da cewa Peter zai lashe Kudu maso Gabas."
"Peter zai lashe Kudu maso Kudu, Peter zai samu ƙuri'un Kiristoci a Arewa, kuma Peter zai samu nasara a yankin Arewa ta Tsakiya."
- Segun Sowunmi
Peter Obi ya ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya buƙaci Bola Tinubu ya mutunta rayukan ƴan Najeriya.
Peter Obi ya shawarcin shugaban ƙasan da ya katse duk abin da yake yi Faransa ya dawo gida Najeriya domin fuskantar matsalolin da suka addabi ƙasar nan.
Jigon na jam'iyyar LP ya nuna cewa ya kamata Tinubu ya dawo gida domin nuna ya damu da rayukan mutanen da ake kashewa a ƙasar nan saboda rashin tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng