Yarjejeniyar da Ke cikin Auren Ronaldo da Sahibarsa Georgina

Yarjejeniyar da Ke cikin Auren Ronaldo da Sahibarsa Georgina

  • Shahararren dan wasan kwallon kafa da ya yi suna, Cristiano Ronaldo da Georgina Rodríguez sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aure da ta tanadi raba kadarorinsu
  • Rahotanni sun ce ma’auratan sun yi bikin aure a birnin Lisbon na kasar Portugal tare da ’ya’yansu da shaidu hudu
  • Sahibar Ronaldo, Georgina za ta ci gaba da amfani da sunan Rodríguez bayan aurensu maimakon na dan wasan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Lisbon, Portugal - Cristiano Ronaldo da abokiyar zamansa ta dogon lokaci, Georgina Rodríguez, sun amince da raba kadarorin da kowannensu ya mallaka kafin aure, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Rahotanni sun ce ma’auratan sun yi aure a wani ƙaramin biki a Lisbon ranar Talata, inda ’ya’yansu da shaidu hudu suka halarta.

Ronaldo ya kulla yarjejeniya da Georgina
Cristiano Ronaldo tare da Georgina Rodriguez Hoto: Cristiano Ronaldo
Source: Facebook

A cewar jaridar Daily Mail, Cristiano Ronaldo da Georgina sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar 10 ga Agusta, kwana guda kafin rahoton bikinsu, a wani ofishin gwamnati da ke Lisbon.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Obi, Kwankwaso sun zauna da yan takarar gwamna 25 a NDC

Yadda za a raba kadarorin

Rahoton ya ce yarjejeniyar ta tanadi cewa kowannensu zai ci gaba da mallakar kadarorinsa daban, ma’ana gidaje da sauran abubuwan da kowannensu ya mallaka kafin aure za su ci gaba da kasancewa mallakinsa na kansa.

Wani kwafin takardar shaidar aurensu da Jornal de Notícias ta wallafa ya kuma bayyana wasu bayanai kan ma’auratan, ciki har da cikakken sunan Ronaldo, shekarunsa da wurin da aka haife shi, da kuma sunayen iyayensa.

An bayyana Georgina, mai shekaru 32, a matsayin wadda aka haifa a Buenos Aires, Argentina, yayin da Ronaldo, mai shekaru 41, aka bayyana shi a matsayin ɗan Madeira, Portugal.

Rahotanni sun nuna cewa mahaifiyar Ronaldo ba ta je wurin ba, amma akwai yar uwarsa cikin wadanda suka halarci bikin.

Georgina za ta riƙe sunanta

Ana kuma sa ran ma’auratan za su ci gaba da amfani da sunayensu na asali bayan aure, inda Georgina za ta ci gaba da amfani da Rodríguez maimakon ɗaukar sunan Ronaldo.

Kara karanta wannan

Soke kudin tsaro da wasu sauye sauye da ADC za ta kawo idan ta ci zaɓen 2027

Rahotanni sun ce Maria Manuel Ferreira de Campos Folhadela de Oliveira ce ta jagoranci bikin auren, bayan da ta yi tafiya daga Porto zuwa Cascais domin gudanar da bikin.

Ronaldo da Georgina sun shafe shekaru suna tare, inda dangantakarsu ta kasance tana jan hankali saboda shaharar ɗan wasan ƙwallon ƙafar da kuma dimbin dukiyar da yake da ita.

Yarjejeniyar aurensu da aka ruwaito ta samar da tsarin doka kan yadda za a tafiyar da kadarorinsu, musamman idan aka samu rabuwa ko wani sauyi a yanayin aurensu.

Ronaldo ya auri sahibarsa
Cristiano Ronaldo tare da sahibarsa Georgina Rodriguez Hoto: Cristiano Ronaldo
Source: Facebook

Alakar Davido da Cristiano Ronaldo

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa shi babban masoyin fitaccen dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo ne.

Fitaccen mawakin dan Najeriya ya kara da bayyana cewa shi da Ronaldo su kan yi magana akai-akai saboda abota da ke tsakaninsu.

mawakin ya ce ya goyi bayan kasar Portugal ta lashe Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026 saboda yana da abokai da dama a cikin tawagar kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng