"Za Ta Fashe": Kusa a PDP Ya Yi Hasashen Hatsarin da ke Tunkaro APC

"Za Ta Fashe": Kusa a PDP Ya Yi Hasashen Hatsarin da ke Tunkaro APC

  • Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya taɓo batun sauya sheƙar da ake yi zuwa APC
  • Wabara ya bayyana cewa sauya sheƙar ba abin mamaki ba ne domin abu ne wanda ya saba faruwa a siyasa
  • Ya bayyana cewa PDP za ta ci gajiyar sauya sheƙar a nan gaba domin rikici zai kunno kai a cikin jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban kwamitin amintattu na PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya yi magana kan sauya sheƙar da wasu jiga-jigan jam'iyyar suka yi zuwa jam'iyyar APC.

Sanata Adolphus Wabara ya bayyana cewa babu dalilin yin fargaba dangane da sauya sheƙar Sanata Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da wasu manyan jiga-jigan PDP zuwa jam’iyyar APC.

Adolphus Wabara
Wabara ya ce APC za ta tarwatse nan gaba Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Shugaban kwamitin amintattun na PDP ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

BOT ta taɓo batun sauya sheƙa a PDP

Tsohon shugaban majalisar dattawan wanda ya amince cewa tabbas PDP za ta yi kewar waɗanda suka sauya sheƙa, duk da haka ya ce wannan sauyin shekar ba zai raunana ƙarfin jam’iyyar ba a zaɓen 2027.

A maimakon haka, ya bayyana cewa sauya sheƙar wani abu ne da zai yi wa jam'iyyar amfani a nan gaba.

Sanata Wabara ya ce APC za ta fuskanci rikici nan ba da jimawa ba sakamakon yawan mambobin PDP da ke sauya sheka zuwa APC, lamarin da zai haifar da danniya ga ƴaƴan APC na asali da suka dade suna gina jam’iyyar.

"PDP za ta ci gajiya daga ƙarshe saboda nan gaba kaɗan, rikici zai tashi a APC. Waɗanda suka sauya sheƙa zuwa APC za su fara ƙoƙarin ƙwace iko daga hannun waɗanda suka daɗe suna gina jam’iyyar."
"Wadanda aka kora daga APC za su fara neman mafaka, kuma tabbas za su dawo PDP."

- Sanata Adolphus Wabara

Sauya sheƙa zuwa APC bai ba Wabara mamaki ba

Wabara, wanda ya ce bai yi mamakin sauyin shekar manyan jiga-jigan PDP ba, ya bayyana cewa sauyin sheƙa a siyasa abu ne da aka saba da shi.

Ya danganta dalilan sauyin shekar da wasu abubuwa kamar yanke shawara ta ƙashin kai, rasa ƙwarin gwiwa ga tsarin zaɓe, da kuma son tabbatar da samun wa'adi na biyu a ofis.

Sanata Adolphus Wabara
Wabara ya ce bai yi mamaki ba kan masu sauya.sheka daga PDP zuwa APC Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook
"Mun daɗe muna sa ran hakan, kuma ina ganin ya kamata mu ƙara sa rai da cewa ƙarin wasu za su biyo baya. Amma ba abin damuwa ba ne. Wannan siyasa ce."
"Mun daɗe muna hasashen irin waɗannan irin sauyin sheƙar kuma mun san dalilansu, wasu domin samun wa'adi na biyu ne, wasu kuma domin neman kariya."

- Sanata Adolphus Wabara

Sanata Wabara ya ƙara da cewa duk da sauyin sheƙar da ake yi, zaɓen 2027 ba zai zama mai sauƙi ga jam’iyya mai mulki ta APC ba.

Shugaban PDP ya magantu kan zaɓen 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum, ya yi magana kan zaɓen 2027.

Umar Damagum ya bayyana cewa zaɓen na 2027 zai kasance ne tsakanin ƴan Najeriya da jam'iyyar APC mai mulki.

Shugaban na PDP ya nuna cewa zaɓen ba zai nuna ƙarfi ko yawan gwamnoni da wata jam'iyya ta ke da su ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng