Allah Ya Tsare: Yadda Abokan Gaba Suka Yi Yunkurin Kashe babban Sarki a Najeriya
- Sarkin masarautar Iwo, Abdulrasheed Akanbi, ya bayyana yadda ya yi nasara kan abokan gaba duk da yunkurin kashe shi sau da dama
- Oluwo ya bayyana cewa ya tsira daga sharrin masu zarge-zarge, jifar aljanu da kuma shirye-shiryen tsige shi daga gadon sarauta
- Sarkin ya bayyana cewa Allah kadai ne garkuwarsa, kuma kariyar da Allah ke ba shi ce ke kare shi fiye da masu tsaron lafiyarsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun – Abdulrasheed Adewale Akanbi, Sarkin Iwo, ya bayyana yadda ya samu nasara kan abokan gaba duk da yunkurin kashe shi da aka yi a lokuta da dama.
Legit.ng ta ruwaito cewa Oluwo ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin, 21 ga Afrilu, lokacin da ya karɓi ɗan damben duniya, Rasheed Idowu ‘Iwo’ wanda aka fi sani da ID Buster, a fadarsa.

Asali: Twitter
Iwo: 'Dan dambe ya ziyarci Sarkin Akanbi
A kwanan nan, ɗan damben Najeriyar ya kare kambunsa na UBO a jihar Legas, inda ya doke ɗan damben Misira, Ahmed Swedy, kamar yadda aka ga bidiyon a shafin Iwoland Hub na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kawo karshen damben ne tun a zagaye na uku bayan Swedy ya miƙa wuya, saboda yawan naushin da ID Buster ke kai masa da ya gaza jurewa.
Kalli bidiyon a nan kasa:
Da yake martani kan nasarar 'ɗan uwansa, Sarki Abdulrasheed Akanbi ya bayyana cewa kamar yadda yake yakar cin hanci da rashawa a gargajiyance, haka ID Buster ke samun nasarori a fagen dambe.
Basaraken ya yi alfahari da izinin hazakar da ID Buster ke nunawa tare da alƙawarin kasancewa a tare da shi a koyaushe domin karfafa masa gwiwa.

Asali: Twitter
"Allah shi ne garkuwata" – Sarkin Iwo
Da yake ba da misali da rayuwarsa, Sarki Akanbi ya bayyana cewa an shirya kashe shi, an yi ƙoƙarin tsige shi da kuma jifarsa da zarge-zargen ƙarya, amma ya yi nasara da ikon Allah.
Sarkin masarautar ta Iwo ya ce:
“Sun turo da motar tirela ta kashe mu. Ko da ta yi karo da mu, ita ce ta faɗi. Na ga lokacin da wani mala'ika yake jan ta. Ku yarda da Allah ɗaya kuma kada ku yi shakku a kan shi.”
Oluwo ya ƙara da cewa:
“Idan ka yarda da Allah ɗaya ne, to Allah zai turo mala'ikunsa domin kare ka koyaushe. Duk da muna da masu tsaron lafiyarmu, amma kariyar Allah ce ke tasiri a kanmu.”
Bugu da ƙari, Oluwo wanda musulmi ne mai tsantseni, ya ce babu wanda zai iya tsige shi daga mukaminsa, yana mai cewa ba zai kauce daga hanyar Allah ba.
Ya ce:
“Zan sake jaddadawa cewa babu wanda zai iya tsige ni. Sun yi ƙoƙari sau da yawa amma sun kasa. Wadanda ke shirya hakan su ne ke shan kasa, kuma za su ci gaba da faduwa.”
Kalli bidiyon Sarki Akanbi da ID Buster da wani Olaitan Abass Oladepo ya wallafa a shafinsa na Facebook a kasa:
Sarki Akanbi ya karya wani tsohon gunki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, babban basarake a jihar Osun, Abdulrasheed Adewale Akanbi, ya bayyana yadda ya karya gunki mai shekaru 800 da ke fadarsa.
Sarkin masarautar Iwo ya nanata cewa ba zai daina adawa da bautar gumaka ba, yana mai bayyana hakan a matsayin hanyar da ba ta kai ga gaskiya ba.
Haka kuma, babban basaraken ya bayyana babban dalilinsa na ci gaba da rungumar addinin Musulunci da gaske a dukkan tafiyarsa ta rayuwa.
Asali: Legit.ng