Matasan Yarabawa Sun Bukaci Sanya Dokar Ta Baci a Zamfara, Sun Fadi Dalili

Matasan Yarabawa Sun Bukaci Sanya Dokar Ta Baci a Zamfara, Sun Fadi Dalili

  • Ana ta samun masu kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta ɓaci a jihar Zamfara saboda matsalar rashin tsaro
  • Ƙungiyar matasan Yarabawa (YYC) ta buƙaci a sanya dokar ta ɓaci a Zamfara domin dawo da zaman lafiya a jihar
  • YYC ta koka kan yadda rikicin siyasa da matsalar rashin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a jihar Zamfara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar matasan Yarabawa (YYC) yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Zamfara domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wannan kiran na sanya dokar ta ɓaci na zuwa ne biyo bayan taɓarɓarewar rikicin siyasa da kuma ƙara tsanantar matsalar tsaro a jihar.

An bukaci sanya dokar ta baci a Zamfara
Kungiyar YƳC ta nemi a sanya dokar ta baci a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban YYC na ƙasa, Eric Oluwole, ya fitar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ake son sanya dokar ta ɓaci a Zamfara?

Ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan ci gaba da rikici tsakanin ɓangarori biyu na majalisar dokokin jihar da kuma rashin ɗaukar mataki daga Gwamna Dauda Lawal.

YYC ta lura cewa a yayin da hare-haren ƴan bindiga, kisan gilla da sace-sacen mutane ke ƙara ƙamari, ƴan majalisa kuma suna ta fafatawa da juna a rikicin siyasa.

Sanarwar ta bayyana cewa yanzu haka akwai majalisu biyu masu zaman kansu a jihar, inda ɗaya daga cikin ɓangarorin ke barazanar tsige Gwamna Dauda Lawal bisa zargin taɓarɓarewar tsaro, tsadar rayuwa da korar ɗumbin ma’aikatan gwamnati.

YYC ta yi gargaɗin cewa matsalar za ta iya ƙara taɓarɓarewa matuka idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

"Mu a ƙungiyar matasa ta Yarabawa muna matuƙar damuwa kan tsanantar rikici da rashin zaman lafiya a Zamfara, wanda rikicin neman iko tsakanin ɓangarori biyu na majalisar dokokin jihar ke haddasawa, yayin da gwamnan ya kasa ɗaukar mataki."

"Abin takaici mafi girma shi ne yadda matsalar tsaro ke ƙara kamari, inda hare-haren ƴan bindiga ke haddasa kashe-kashe da garkuwa da mutane babu kakkautawa, yayin da ƴan majalisa ke yin rikicin siyasa."

- Eric Oluwole

YYC ta koka kan rashin tsaro a Zamfara

Dauda Lawal
YYC na son a ayyana dokar ta baci a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

YYC ta kuma koka da cewa a cikin watanni biyar da suka gabata kaɗai, aƙalla mutane 41 ne aka kashe, fiye da 185 kuma aka sace a jihar Zamfara.

"Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankunan suna rayuwa cikin fargaba, inda masu dauke da makamai ke tilasta musu biyan maƙudan kudade domin kare rayukansu."
"A saboda haka, domin dakile cigaban wannan rikici da kuma kauce wa jefa jihar cikin ruɗani gaba ɗaya, muna kira da a gaggauta ayyana dokar ta-baci a Zamfara domin dawo da doka da oda."

- Eric Oluwole

Ƙungiyar NCAJ ta buƙaci sa dokar ta ɓaci a Zamfara

A wani labari kuma, kun ji cewa ana ci gaba da kira ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu da ta ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara.

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama a Arewa (NCAJ), ta bi sahun masu yin wannan kiran inda ta bukaci Shugaba Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a jihar.

NCAJ ta ce ɗaukar matakin ya zama dole saboda tabarbarewar tsaro, rushewar dimokuraɗiyya, da zargin haɗin kai tsakanin jami’an gwamnati da masu hakar ma’adanai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng