'Yan Boko Haram Sun kai Harin Ta'addanci bayan Zuwan Ministan Tsaro a Borno

'Yan Boko Haram Sun kai Harin Ta'addanci bayan Zuwan Ministan Tsaro a Borno

  • Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai harin ta'addanci a wani ƙauye da ke ƙaramar hujumar Gwoza ta jihar Borno
  • Tsagerun sun hallaka ƴan sa-kai mutum biyu tare da wasu masu yin itace bayan sun yi musu kwanton ɓauna
  • Sarkin Gwoza ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya buƙaci hukumomi da su ƙara tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Wasu ƴan ta'adda da ake zargin na Boko Haram ne sun kai harin ta'addanci a jihar Borno.

Ƴan ta'addan na Boko Haram sun kashe ƴan sa-kai mutum biyu tare da wasu masu yin itace a ƙauyen Bokko Ghide, da ke ƙaramar hukumar Gwoza, ta jihar Borno.

'Yan Boko Haram sun kai hari a Borno
'Yan Boko Haram sun kashe mutum 12 a Borno Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

Mai Martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, ya tabbatar da faruwar lamarin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan Boko suka yi ta'asa a Borno

Alhaji Mohammed Shehu Timta ya bayyana cewa an yi wa ƴan sa-kan kwanton ɓauna ne a kan hanyar Kirawa, da ke yankin Pulka, inda aka kashe su.

Haka kuma ya bayyana cewa sauran mutane 10 da aka kashe, su ne waɗanda suka shiga daji domin neman itacen girki.

"Sun tafi cikin wani daji da ke kusa domin nemo itacen wuta a ranar Asabar, inda ƴan ta'addan suka yi musu kwanton bauna suka kashe 10 daga cikinsu, sannan suka bar guda biyu da munanan raunuka."
"Mun riga mun birne gawarwakin mutum 10 kuma mun ɗauki wadanda suka samu raunuka zuwa Maiduguri domin samun kulawar likita."

- Alhaji Mohammed Shehu Timta

Sarkin ya bayyana baƙin cikinsa kan kashe ƴan sa-kai guda biyu da suka sadaukar da rayukansu domin kare rayukan mutane a ranar Juma’a.

Ya yi addu’ar Allah Ya saka musu da Aljannatul Firdaus, ya kuma bai wa iyalansu da al’ummarsu haƙurin jure wannan babban rashi.

An yabawa mahukunta

Hakazalika, Sarkin ya yabawa gwamnatin jihar Borno da dakarun soji saboda kokarin da suke yi wajen yaki da ƴan ta'addan Boko Haram fiye da tsawon shekara 10.

"Sun kasance suna iyakar ƙoƙarinsu wajen shawo kan rikicin. Muna kuma kira ga sojoji da su fara amfani da sabbin hanyoyin fasaha na yaki kamar amfani da jiragen sintiri marasa matuƙi, da sauran makaman zamani domin kawo ƙarshen rikicin."

- Alhaji Mohammed Shehu Timta

Yan Boko Haram sun kai hari a Borno
'Yan Boko Haram sun kashe mutane a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Sarkin ya kara da cewa damina na gabatowa, amma ƙaruwar hare-hare ya fara razana mutane a yankin.

"Mutane yanzu suna tsoron shiga gonakinsu, alhali kuma lokaci ne na shirya gonakin noma kafin ruwan sama ya sauka sosai."

- Alhaji Mohammed Shehu Timta

Wannan harin dai ya faru ne ƙasa da sa’o’i 48 bayan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura ministan tsaro, Badaru Abubakar, da babban hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa, da wasu manyan hafsoshin soja zuwa Borno domin tantance halin tsaro a jihar.

Yadda ƴan Boko Haram ke samun makamai

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai sharhi kan al'amuran jama'a, Bulama Bukarti ya yi magana kan hanyoyin da ƴan ta'adda ke samun makamai.

Bulama Bukarti ya bayyana ƴan bindiga da ƴan ta'addan Boko Haram na samun makamai ne ta hanyar tara kuɗaden fansa.

Ya bayyana cewa babbar hanyar samun kuɗaɗe ga tsagerun ita ce karɓar kuɗaɗen fansa daga hannun ƴan uwan waɗanda suka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng