'Yan PDP a Majalisar Tarayya Sun Fadi Matsayarsu kan Tazarcen Tinubu a 2027
- Ƙungiyar ƴan majalisar tarayya na jam'iyyar PDP a jihar Rivers, ta amince da sake goyawa Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027
- Mambobin ƙungiyar sun bayyana cewa za su yi aiki tuƙuru domin ganin shugaban ƙasan ya sake samun mulki a karo na biyu
- Sun godewa shugaban ƙasan kan yadda yake yabawa da irin ƙoƙarin da Nyesom Wike yake yi a muƙaminsa na ministan Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Mambobin ƙungiyar ƴan majalisar tarayya na jihar Rivers na jam'iyyar PDP sun bayyana matsayarsu kan tazarcen mai girma Bola Tinubu a 2027.
Ƴan majalisar sun bayyana cikakken goyon bayansu ga takarar shugaban ƙasa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa wacce dukkan mambobin suka sanyawa hannu da Sanata Barry Mpigi ya karanta a ranar Asabar a birnin Port Harcourt, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan PDP sun goyi bayan tazarcen Tinubu
Mambobin ƙungiyar sun bayyana cewa nasarorin da gwamnatin Tinubu ke nunawa a fili ne suka sanya su yanke wannan hukunci, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Ƴan majalisar sun yabawa manufofin tattalin arziƙi na Tinubu, inda suka ce an tsara su ne domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan da ke fama da matsaloli.
Ƙungiyar wacce ta ƙunshi sanatoci biyu da mambobi bakwai na majalisar wakilai, dukkansu ƴan jam’iyyar PDP, sun buƙaci sauran masu sha’awar takara da Tinubu a 2027 da su ajiye burinsu.
"Mu mambobin majalisar tarayya daga jihar Rivers, ciki har da Sanatoci da ƴan majalisar wakilai, muna miƙa godiyarmu ta musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da kuma yarda da jajirtaccen jagoranmu, Nyesom Ezenwo Wike."
"Muna godiya a garesa kan yabon da ya yi a fili kan hazaƙar ministan babban birnin tarayya, wanda ya bayyana shi a matsayin shugaban samar da ababen more rayuwa."

Asali: Facebook
"Mun yi aiki tuƙuru ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike domin ganin nasarar zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Kuma mun samu nasara a wannan aiki."
"A matsayinmu na mambobin majalisar tarayya daga jihar Rivers, mun bayyana a fili cewa mun yanke shawarar marawa Tinubu baya ba tare da wani sharaɗi ba domin sake samun nasara a zaɓen 2027."
“Kamar yadda muke mafi kusa da jama'a a matsayinmu na ƴan majalisa, za mu fara gagarumin aikin wayar da kai da ƙwadaitar da mutanenmu domin sake maimaita nasarar da muka samu a 2023 domin tabbatar da sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu."
- Sanata Barry Mpigi
Jam'iyyar PDP ta ƙara hargitsewa da rikici
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ƙara samun kanta cikin rikicin shugabanci a jihohin Bayelsa da Edo.
Rikicin ya samo asali ne bayan mambobin PDP masu biyayya ga Nyesom Wike sun naɗa shugabanni a jihohin guda biyu.
PDP dai ta rabu gida biyu a yankin inda akwai ɓangaren da Wike ke marawa baya da kuma wanda kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ya amince da shi.
Asali: Legit.ng