Aminu Ado Bayero Ya Ci Gaba da Sarauta, Ya Nada Sanusi Sabon Galadiman Kano

Aminu Ado Bayero Ya Ci Gaba da Sarauta, Ya Nada Sanusi Sabon Galadiman Kano

  • Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ɗaga darajar sarautar yayansa Alhaji Sanusi Ado Bayero daga Wamban Kano
  • Alhaji Aminu Ado Bayero ya naɗa Sanusi Ado Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano bayan taron majalisar masarautar Kano
  • Naɗin na sa na zuwa ne bayan rasuwar tsohon Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi wanda ya rasu bayan ya yi fama da jinya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Bayanai sun zo cewa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa Galadiman Kano.

Aminu Ado Bayero ya naɗa ƴaƴansa, Alhaji Sanusi Ado Bayero, a matsayin sabon Galadiman Kano bayan rasuwar Abbas Sanusi.

Aminu Ado Bayero ya nada Galadiman Kano
Aminu Ado Bayero ya nada yayansa a matsayin Galadiman Kano Hoto: Masarautar Kano New Media
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa naɗin Alhaji Sanusi Ado Bayero ya zo ne ta cikin wata wasiƙa da babban jami’in gudanarwa na masarautar, Alhaji Awaisu Abbas Sanusi, ya sanyawa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminu Ado ya naɗa Galaɗiman Kano

An fitar da wasiƙar ne bayan wani taron majalisar masarautar Kano da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya jagoranta a ranar Laraba, 16 ga Afrilu, 2025.

Jaridar Leadership ta ce an bayyana a cikin wasiƙar cewa za a yi naɗin na sabon Galadiman Kano ne a ranar Juma'a, 2 ga watan Mayun 2025.

Marigayi Abbas Sanusi, babban dattijo da ake girmamawa a masarautar Kano, ya rasu a watan Maris 2025 bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Rasuwar Abba Sanusi ta jawo an bar ɗaya daga cikin manyan sarauta masu daraja a masarautar babu mai riƙe da ita.

Wanene Sanusi Ado Bayero?

Sanusi Ado Bayero, wanda tun da farko mahaifinsu, marigayi Sarki Ado Bayero, ya naɗa a matsayin Ciroman Kano kuma Hakimin Gwale, an ɗauke shi a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa bayan rasuwarsa a shekarar 2014.

Sai dai, Sanusi Lamido Sanusi, aka naɗa a matsayin Sarkin Kano, wanda hakan ya sa Sanusi Ado Bayero ya bar Kano domin nuna rashin jin daɗinsa.

Bayan sake fasalin tsarin masarautar Kano da kuma hawan Aminu Ado Bayero a matsayin Sarki a watan Yulin 2020, an mayar da Sanusi Ado Bayero cikin majalisar masarautar a matsayin Wamban Kano.

Sanusi Ado Bayero lauya ne wanda ya kammala karatunsa kuma mamba ne na ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya tun daga shekarar 1984.

Ya yi aiki a gwamnatin jihar Kano, inda ya kai matsayin babban sakatare. Daga bisani, ya zama manajan darakta na hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA) kafin a tsige shi a shekarar 2015.

Sanusi Ado Bayero
Sanusi Ado Bayero ya zama Galadiman Kano Hoto: Masarautar Kano New Media
Asali: Facebook

Sanusi II ya nada Galadiman Kano

Abin lura shi ne, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, shi ma ya naɗa Mannir Sanusi a matsayin Galadiman Kano.

Hakan alama ce da ke nuna har obe akwai rarrabuwar kai a tsakanin ɓangarorin biyu masu iƙirarin riƙe da masarautar Kano.

Tasirin masarautar Kano a Arewa

Masarautar Kano na daga cikin fitattun masarautun gargajiya a Najeriya, mai dogon tarihi da tasiri a harkokin siyasa da zamantakewar Arewa.

Sarautun da ake naɗa wa a cikin masarautar, kamar Galadima, na taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da harkokin masarautar da kuma kula da al'umma.

A cikin shekarun da suka gabata, masarautar ta fuskanci manyan sauye-sauye da suka hada da sauya sarki da sake fasalin tsarin masarauta.

Bayan rasuwar tsohon Sarkin Kano, Ado Bayero, a shekarar 2014, masarautar ta shiga wani sabon yanayi na sauyi, inda aka naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki, lamarin da ya haifar da sabani tsakanin manyan iyalan masarautar.

Daga baya, a shekarar 2020, bayan sauke Muhammadu Sanusi II da hawan Aminu Ado Bayero, an sake jaddada tsarin shugabanci a masarautar.

Wannan sabon naɗin da Sarkin Kano na yanzu, Aminu Ado Bayero, ya yi wa Sanusi Ado Bayero zuwa matsayin Galadiman Kano, na zuwa ne a wani lokaci da ake ƙoƙarin farfado da haɗin kan masarautar bayan wasu shekaru na rarrabuwar kai da rikice-rikice.

Naɗin ya kuma biyo bayan mutuwar tsohon Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda ke da gagarumar matsayi a cikin majalisar masarautar.

Aminu Ado Bayero ya yabi Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kwararo yabo ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Sarkin na Kano ya yabi Shugaba Tinubu ne saboda kafa hukumar raya kiwo da makiyaya ta ƙasa da ya yi.

Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa kafa hukumar zai tabbatar da zaman lafiya a Arewacin Najeriya tare da sauya rayuwar Makiyaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng