'Yan Bindiga Sun Farmaki Matafiya, Sun Yi Awon Gaba da Fasinjoji

'Yan Bindiga Sun Farmaki Matafiya, Sun Yi Awon Gaba da Fasinjoji

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan matafiya waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba a jihar Zamfara
  • Miyagun ƴan bindigan sun kashe direban motar bayan sun buɗe musu wuta a kan hanyar Bagaga zuwa Anka da safiyar ranar Asabar
  • Bayan kashe direban motar, ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da fasinjojin da ke cikinta zuwa cikin daji
  • Jami'an tsaro sun fara yunƙurin ganin sun kuɓutar da mutanen da aka sace cikin ƙoshin lafiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki kan matafiya da ke tafiya a cikin wata mota ƙirar Golf a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan waɗanda suka kai harin a ranar Asabar, 26 ga watan Afrilu, 2025, a hanyar Bagaga zuwa Anka, sun kashe direban motar sannan suka yi garkuwa da fasinjoji biyar.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan sun sace fasinjoji a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kai wa matafiya hari

Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:40 na safe, lokacin da ƴan bindigan suka tare hanyar tare da buɗe wuta kan motar.

Harbin da suka yi ya yi sanadin mutuwar direban motar, yayin da suka yi awon gaba da fasinjoji guda biyar da ke cikin motar.

Bayan samun rahoton wannan mummunan lamari, rundunar hadin gwiwa ta jami'an tsaro ta hanzarta tura dakarunta zuwa wajen da abin ya faru domin daƙile ci gaba da aukuwar ɓarna.

An garzaya da direban motar da aka harba zuwa asibitin da ke Bagaga domin samun kulawa cikin gaggawa, duk da cewa daga bisani ya rasu.

Jami'an tsaro sun fara ƙoƙarin ceto mutane

A halin yanzu, jami'an tsaro sun shiga cikin dazuka da wuraren da ake zargin ƴan bindigar suka fake domin ceto wadanda aka sace.

Ana ci gaba da gudanar da bincike da kuma daukar matakan da suka dace domin gano inda ƴan ta'addan suke da kuma kuɓutar da mutanen da ke hannunsu cikin ƙoshin lafiya.

'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara
'Yan bindiga sun kashe direba a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wannan harin ya ƙara jefa al’umma cikin fargaba da damuwa, musamman ma a wannan lokaci da hare-haren ƴan bindiga ke kara tsananta a wasu yankunan jihar Zamfara.

Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an kama wadanda suka aikata wannan aika-aika domin su fuskanci hukunci.

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-hare a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.

Miyagun ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a wasu ƙauyuka guda uku na ƙaramar hukumar Maru da ke Zamfara.

A yayin hare-haren, ƴan bindigan sun hallaka mutane 28 ciki har da wasu masu haƙar ma'adanai bayan sun buɗe musu wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng