An Fara Rokon 'Yan Arewa kan Tazarcen Shugaba Tinubu a 2027

An Fara Rokon 'Yan Arewa kan Tazarcen Shugaba Tinubu a 2027

  • Government Tompolo wanda aka fi sani da Tompolo ya buƙaci ƴan Arewa su goyi bayan tazarcen shugaban ƙasa Bola Tinubu a 2027
  • Tsohon shugabaɓ na tsagerun Niger Delta ya bayyana cewa Tinubu mutumin kirki ne kuma ya cancanci ya yi shekara takwas a kan mulki
  • Tompolo ya nuna cewa zai karaɗe jihohin Arewa 19 domin neman goyon baya ga Shugaba Tinubu
  • Ya bayyana shugaban ƙasan a matsayin mutumin kirki wanda yake da ƙwarewa da gogewar da za su yi wa Najeriya amfani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban tsagerun Niger Delta, Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ya yi kira ga shugabannin siyasa na Arewa da su marawa Shugaba Bola Tinubu baya domin sake samun nasara a zaɓen 2027.

Tompolo, wanda kwanan nan ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu domin ci gaba da mulki, ya bayyana shugaban ƙasan a matsayin mutum nagari kuma mai ƙwarewa da gogewa da za ta kai Najeriya ga gaci.

Tompolo ya roki 'yan Arewa kan Tinubu
Tompolo ya bukaci 'yan Arewa su bari Tinubu ya yi shekara 8 Hoto: Government Tompolo, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Government Tompolo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tompolo ya yi kira ga ƴan Arewa kan tazarcen Tinubu

A cikin kiran da ya yi wa yankin Arewa, Tompolo ya ce kamata ya yi a bar Tinubu ya kammala shekaru takwas a mulki kamar yadda tsohon shugaban ƙasa ɗan Arewa, Muhammadu Buhari, ya yi.

Tsohon shugaban tsagerun ya yi alƙawarin yin tafiye-tafiye zuwa dukkan jihohin Arewa domin roƙon mutanen yankin su marawa Tinubu baya a yunƙurinsa na samun wa’adi na biyu.

"Za mu yi namu ƙoƙarin, har ma mu fita daga yankunanmu zuwa yankin Arewa don tattaunawa da ƴan uwammu domin samun goyon baya ga wa'adinsa na biyu."
"Tinubu mutum ne nagari, kuma yana da kwarewar da za ta ɗaukaka wannan ƙasa."
"Ina shirin yin tafiye-tafiye zuwa dukkan jihohin Arewa domin roƙonsu. Buhari ya shafe shekaru takwas a mulki yanzu. Don haka, ba ma buƙatar wani ya jefa ƙasar nan cikin ruɗani."

"Mu bar Tinubu ya kammala shekarunsa takwas, sannan mu nemi wani sabon shugaba. Babu dalilin da zai sa wani ya riƙa tunanin mulki mallakin wani yanki ne kawai."
"Dole ne mu ba Tinubu damar kammala shekarunsa takwas, za mu yi kira ga kowa, kuma da ikon Allah kowa zai goyi bayansa."

Government Tompolo

Government Tompolo
Tompolo ya bukaci a bar Tinubu ya yi shekara 8 a mulki Hoto: Government Tompolo
Asali: Facebook

Tompolo ya kuma jaddada cewa sarakunan gargajiya na Jihar Delta sun amince da sake zaben Shugaba Tinubu.

Ƴan majalisun PDP sun goyi bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƴan majalisar tarayya na PDP a jihar Rivers ta nuna goyon bayansu ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Ƙungiyar wacce ta ƙunshi sanatoci da ƴan majalisar wakilai ta nuna cikakken goyon bayan ta ga tazarcen Tinubu a 2027.

Ƴan majalisar sun kuma yi kira ga duk masu son karawa da Tinubu a zaɓen 2027, da su haƙura su ajiye burinsu na yon takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng