'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Farmaki Jami'an Tsaro a Adamawa, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Farmaki Jami'an Tsaro a Adamawa, an Samu Asarar Rayuka

  • Ƴan ta'addan Boko Harsm ɗauke da makamai sun yi ta'addanci a jihar Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya
  • Miyagun ƴan ta'addan sun hallaka mafarauta da ƴan sa-kai na CJTF har guda 10 a ƙauyen Kwabre na ƙaramar hukumar Hong
  • Shugaban ƙaramar hukumar Hong ya tabbatar da batun kai harin, wanda ya ce an yi ta'adin ne da yammacin ranar Asabar
  • Ya ce ƴan ta'addan da ake zargin Boko Haram ne sun kuma ƙona gidaje masu yawa tare da lalata amfanin gona da aka ajiye

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - Ƴan ta'adda da ake zargin na Boko Haram ne sun kashe mafarauta a jihar Adamawa.

Ƴan ta'addan sun hallaka mafarautan ne tare da ƴan ƙungiyar sa-kai na CJTF guda 10 a ƙauyen Kwapre da ke ƙaramar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

'Yan Boko Haram sun kai hari a.Adamawa
'Yan Boko Haram sun kashe mafarauta a Adamawa Hoto: @GovernorAUF
Asali: Facebook

Shugaban ƙaramar hukumar Hong, Honarabul Usman Wa'aganda, ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Leadership a wata hira da suka yi ta wayar tarho a ranar Lahadi a Yola, babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Boko Haram sun yi ta'asa a Adamawa

Usman Wa'aganda ya bayyana cewa wani mutum ɗaya da ya samu munanan raunuka sakamakon harin na ƴan ta'addan Boko Haram yana karɓar magani a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.

"Ƴan ta'addan Boko Haram sun kashe mafarauta guda 10 a ƙauyen Kwapre a ranar Asabar."
"Wannan ƙauye na Kwapre sau da dama yana fuskantar hare-haren da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi."

- Usman Wa'aganda

Ya kara da cewa maharan sun ƙona gidaje da dama tare da lalata amfanin gona da aka adana.

Usman Wa'aganda ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kara tura jami'an tsaro masu yawa zuwa yankin domin daƙile hare-haren da suka zama ruwan dare.

Ya bayyana cewa maharan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a ranar Asabar, inda suka ƙona gidaje da dama tare da haifar da ruɗani da firgici a tsakanin mazauna yankin.

'Yan Boko Haram sun kashe mutane a Adamawa
'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Adamawa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Boko Haram sun kashe jami'an tsaro

Bisa rahotannin wasu majiyoyi, an bayyana cewa mambobin ƙungiyar CJTF da aka kashe sun fito ne daga ƙaramar hukumar Hawul a jihar Borno.

Mafarautan kuma da suke taimakawa wajen yaƙi da ƴan ta’addan sun fito ne daga wasu ƙananan hukumomin jihar Adamawa.

Usman Wa'aganda ya ce sun ɗauki matakin hada kai da jami’an tsaro domin karfafa yaki da ƴan ta'addan da ke addabar yankin tare da ba da kariya ga rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ƴan Boko Haram sun kai hari a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan jami'an tsaro a jihar Borno.

Miyagun ƴan ta'addan sun hallaka ƴan sa-kai mutum biyu bayan sun yi musu kwanton ɓauna a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Gwoza.

Hakazalika, ƴan ta'addan sun hallaka wasu mutane da suka shiga cikin daji domin neman itace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng