Malamin Addini Ya Yi Hasashen wanda zai Gaji Tinubu a Shugaban Kasa
- Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya yi magana kan siyasar Najeriya
- Primate Ayodele ya bayyana cewa Nuhu Ribadu zai gaji Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shekarar 2031 bayan ya kammala wa'adinsa na biyu
- Malamin addinin ya ja kunnen ƴan Najeriya kan su yi taka tsantsan da ƴan siyasar da ke ƙoƙarin kafa haɗakar ƴan adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya yi magana kan zaɓen shugaban ƙasa.
Primate Ayodele ya yi hasashen cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, zai zama shugaban Najeriya na gaba.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Primate Ayodele ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waye zai gaji Tinubu?
Malamin addinin ya bayyana cewa Ribadu ne zai gaji Tinubu bayan ya kammala wa'adinsa na biyu.
Primate Ayodele ya bayyana cewa Nuhu Ribadu zai zama shugaban ƙasa bayan kammala wa'adi na biyu na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2031.
"Bayan Tinubu, Nuhu Ribadu ne zai karɓi mulki."
- Primate Elijah Ayodele
Haka kuma, ya yi iƙirarin cewa yawancin gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam’iyyar PDP za su kyale ɗan takararsu na shugaban ƙasa su goyi bayan tazarcen Tinubu a 2027.
“Yawancin waɗannan gwamnonin PDP ba za su tsaya tare da dan takararsu na shugaban ƙasa ba."
- Primate Elijah Ayodele
Primate Ayodele ya taɓo batutuwan siyasa
Dangane da batun siyasa a wasu jihohi, Primate Ayodele ya yi hasashen cewa APC ba za ta ci nasara a zanen gwamna na jiihar Anambra ba, yana mai jaddada cewa Gwamna Chukwuma Soludo na ci gaba da samun karɓuwa a wajen al’umma.
Game da shirye-shiryen haɗakar ƴan adawa da ke gudana, malamin addinin ya gargadi ƴan Najeriya da ka da su bari a yaudare su.
Ya bayyana cewa goyon bayan mutane irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai, Bala Mohammed, da Seyi Makinde zai ƙara taɓarɓarar da halin da ƙasar nan ke ciki.
“Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai, Bala Mohammed, da Seyi Makinde za su kara wahalar da rayuwar ƴan Najeriya fiye da irin wahalar da suke fuskanta yanzu ƙarƙashin Tinubu."
"Zaɓen kowane daga cikin waɗannan ƴan siyasa a zaɓe mai zuwa zai haifar da mummunan sakamako. Ya kamata ƴan Najeriya ka da su yi tunanin zaɓen kowane daga cikinsu. Maimakon haka, su ci gaba da marawa Tinubu baya."
- Primate Ayodele

Asali: Facebook
A ƙarshe, Primate Ayodele ya shawarci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri, inda ya bayyana cewa wa'adin mulki na biyu na Tinubu zai fi na farko kyau.
"Wa'adin mulki na biyu na Tinubu zai fi na farko kyau. Tinubu da ya kai Najeriya wannan matsayi, kuma shi ne zai fito da ƙasar daga cikin halin da take ciki a wa’adinsa na biyu. Ya kamata ƴan Najeriya su kai zuciya nesa."
- Primate Elijah Ayodele
Tompolo ya roƙi ƴan Arewa kan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban tsagerun Niger Delta, Government Ekpemupolo, ya nemi alfarmar ƴan Arewa kan tazarcen Shugaba Bola.Tinubu.
Tompolo ya roƙi ƴan Arewa da su marawa Shugaba Bola Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.
Ya bayyana cewa Tinubu mutumin kirki ne kuma ya kamata ya yi shekara takwas kamar yadda Muhammadu Buhari ya yi.
Asali: Legit.ng