Shirin Bola Tinubu da Wike kan Gwamna Fubara da Aka Dakatar
- Tsohon shugaban tsagerun Niger Delta, Government Ekpemupolo wanda aka fi sani da Tompolo ya yi magana kan rikicin siyasar jihar Rivers
- Tompolo ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu da Nyesom Wike na ƙoƙarin dawo da Gwamna Siminalayi Fubara wanda aka dakatar
- Ya bayyana cewa dukkanin ɓangarorin da abin ya shafa, suna ƙoƙarin ganin an warware rikicin siyasar jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ya ce Shugaba Bola Tinubu da Nyesom Wike, suna ƙoƙari sosai don dawo da Siminalayi Fubara a matsayin gwamnan jihar Rivers.
Tompolo shi ne shugaban Tantita Security Services Nigeria Limited, wani kamfani mai kula da tsaron bututun man fetur da ke yaƙi da satar ɗanyen mai a jihar Rivers da sauran yankunan Niger Delta.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Tompolo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya dakatar da Fubara
A ranar 18 ga watan Maris, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers, yana mai cewa rikicin siyasa da ya daɗe yana gudana ne ya sa aka ɗauki wannan mataki.
Shugaban ƙasan ya kuma dakatar da Gwamna Fubara daga muƙaminsa, tare da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da kuma dukkan mambobin majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Tinubu ya naɗa Ibok-Ete Ibas, tsohon hafsan rundunar sojan ruwa, a matsayin shugaban riƙon kwarya na jihar Rivers.
Shirin Tinubu kan Fubara
Da yake magana kan halin da ake ciki, Tompolo ya bayyana cewa Fubara zai dawo nan bada dadewa ba a matsayin gwamnan Rivers.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin sulhunta rikicin tsakanin dukkan ɓangarorin da abin ya shafa dangane da dakatar da gwamnan.
"Gwamnan da aka zaba ta hanyar doka a jihar Rivers yana kan hanyarsa ta dawowa."
"Matsalar da ke tsakanin Wike da Fubara tamkar tsakanin yaro ne da ubangidansa. Shugaban ƙasarmu mutum ne da ke kare dimokuradiyya, kuma babu wani yunƙuri daga gare shi na rushe ta."
"Muna yin duk abin da ya kamata, har da shugaban ƙasa da Wike, domin dawo da Fubara a matsayin gwamna."
- Government Ekpemupolo

Asali: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa Fubara ya gana da Shugaba Tinubu a birnin Landan a farkon watan Afrilu.
A lokacin tattaunawarsu, an ruwaito cewa Fubara ya amince zai yi wasu abubuwa domin warware rikicin siyasar da ya addabar jihar Rivers.
An roƙi ƴan Arewa kan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Government Ekpemupolo wanda aka fi sani da Tompolo ga roƙi ƴan Arewa kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu.
Tsohon shugaban tsagerun Niger Delta, ya buƙaci ƴan Arewa da su bari Tinubu ya yi shekara takwas kamar Muhammadu Buhari.
Tompolo ya nuna cewa shugaban ƙasan mutumin kirki ne wanda yake da ƙwarewar da ake buƙata domin kawo ci gaba ga Najeriya.
Asali: Legit.ng