Jarrabawar UTME: JAMB Ta Yi Wa Peter Obi Martani kan Wahalar da Dalibai

Jarrabawar UTME: JAMB Ta Yi Wa Peter Obi Martani kan Wahalar da Dalibai

  • JAMB ta yi martani ga tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, kan kalamansa bisa yadda tsarin jarrabawarta
  • Hukumar JAMB ta bayyana cewa ƙarfe 8:00 na safe take fara gudanar da jarabawarta saɓanin ƙarfe.6:00 da Peter Obi ya yi iƙirari
  • Tun da farko dai Obi ya nuna damuwa kan yadda ake tursasa yara masu ƙananan shekaru fitowa daga gidajensu domin zuwa rubuta jarabawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar JAMB ta yi magana kan ƙorafin da Peter Obi ya yi kan wahalar da ɗalibai masu rubuta jarabawar UTME.

Hukumar JAMB wacce ke shirya jarabawar ta UTME ta bayyana cewa yadda ɗan takarar shugaban ƙasan yake tunani ba haka lamarin yake ba.

JAMB ta yi wa Peter Obi martani
JAMB ta yi martani ga Peter Obi Hoto: @JAMBHQ, @Peterobi
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin martanin da hukumar JAMB ta yi wa Peter Obi a shafinta na X a daren ranar Lahadi, 27 ga watan Afirilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya ce JAMB na wahalar da ɗalibai

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, ya nuna damuwa kan yadda ake wahalar da dalibaiasu rubuta jarabawar UTME a Najeriya.

Peter Obi ya koka kan tsarin da hukumar JAMB ta fito da shi na tilastawa ɗalibai masu ƙananan shekaru fitowa daga gidajensu da sassafe domin zuwa rubuta jarabawa.

Ya nuna cewa tsarin sanyawa ƙananan yaran yin jarabawa d aƙarfe 6:00 na safe babban abin kunya ne kuma barazana ce ga lafiyarsu.

Wane martani hukumar JAMB ta yi?

Sai dai, a martanin da hukumar JAMB ta yi, ta bayyana cewa ba ƙarfe 6:00 na safe take fara gudanar da jarabawarta ba.

Hukumar ta bayyana cewa ana fara jarabawar ne da misalin ƙarfe 8:00 na safe saɓanin ƙarfe 6:00 da Peter Obi ya ce ana farawa ba.

Hukumar JAMB
JAMB ta ce ba karfe 6:00 na safe take fara jarabawa ba Hoto: @JAMBHQ
Asali: Twitter

Sai dai, hukumar ta amince cewa tana fara aikin tantance ɗalibai da sauran wasu shirye-shirye da ƙarfe 6:30 na safe.

"@PeterObi muna son jaddada cewa, jarabawarmu tana farawa ne da ƙarfe 8:00 na safe, ba karfe 6:00 na safe ba."
"Duk da cewa tantancewa da sauran shirye-shirye na farawa da ƙarfe 6:30 na safe, yana da matukar muhimmanci a ba wa ɗalibai isasshen lokaci su natsu kafin a fara jarabawa."
"La'akari da yadda galibin ƴan Najeriya ke makara idan aka sanya lokacin farawa ba tare da tanadin jinkiri ba, wannan tsarin jadawalin yana da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da cewa dukkan ɗalibai sun samu isasshen lokaci sun shirya don yin jarabawa yadda ya kamata."

- Hukumar JAMB

Gwamnatin Abba ta raba fam ɗin JAMB kyauta

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta sauƙaƙawa ɗaliban sakandare masu son rubuta jarabawar neman shiga jami'a.

Gwamnatin ta raba fam ɗin JAMB guda 10,000 kyauta ga ɗalibai a makarantun sakandare da ke faɗin jihar.

Wannan matakin dai zai tallafawa ɗalibai masu ƙaramin ƙarfe samun damar rubuta jarabawar JAMB a sauƙaƙe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng