Dakatar da Fubara: Wike Ya Lissafo Sharuddan Samun Zaman Lafiya a Rivers

Dakatar da Fubara: Wike Ya Lissafo Sharuddan Samun Zaman Lafiya a Rivers

  • Ministan harkokin babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya taɓo batun rikicin siyasar da ya addabi jihar Rivers
  • Wike ya bayyana cewa dole ne a nuna da gaske ake yi wajen ganin an samu zaman lafiya a tsakanin ɓangarorin biyu masu rikici
  • Ministan ya bayyana cewa zanga-zangar da ake sanyawa mata na yi, ba za ta sa a dawo da shugabannin da aka dakatar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan hanyar samun zaman lafiya a jihar Rivers.

Nyesom Wike ya bayyana cewa babu irin sharri da ɓata sunan da za a yi da zai kawo zaman lafiya a jihar Rivers.

Nyesom Wike da Fubara
Wike ya ce sai an zauna kan teburin sulhu kafin a samu zaman lafiya a Rivers Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Wike ya faɗi hakan ne yayin wani taron da ka shirya domin murnar cika shekaru 70 na wani tsohon dan majalisar tarayya, Ken Chikere, a garin Port Harcourt, ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanne sharuɗɗa Nyesom Wike ya kafa?

Domin zaman lafiya ya tabbata a jihar, Wike ya ce dole ne a sanya dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da ƴan majalisar tarayya, tare da gaskiya da riƙon amana.

Ya bayyana cewa ayyana dokar ta-baci ya hana aukuwar manyan fitintinu da bala’o’i a jihar.

Ministan na babban birnin tarayya Abuja ya ce yawan zanga-zangar da ake yi a jihar ba zai dawo da shugabannin da aka dakatar ba.

Ya zargi sarakunan gargajiya da sauran shugabanni da cewa sun nuna son kai wajen shiga rikicin siyasar jihar.

Wike ya ce sarakunan ba su yi wani sahihin ƙoƙari na sulhunta bangarorin dake rikici ba, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa abin da zai kawo zaman lafiya a jihar shi ne yin sulhu na gaskiya tsakanin ɓangarorin da ke rikici, ba tare da la'akari da jam'iyyunsu ko ra’ayoyinsu na siyasa ba.

Wike ya taɓo batun sulhu a jihar Rivers

“Babu bukatar a tozarta matanmu su fito tsirara a waje. Irin wannan abu ba zai kawo zaman lafiya ba. Babu irin sharrin da za a yi da zai kawo zaman lafiya."
"Abin da zai kawo zaman lafiya shi ne a nuna ƙasƙantar da kai, a ce saboda jihar nan, muna so kowa ya haɗa kai a yi aiki tare."
“Idan kana da gaskiya, mutane za su gane. Wasu sun yi ƙoƙarin zuwa wajena, na karɓe su hannu bibbiyu. Ban kore su ba. Amma kawai gani na ba zai kawo zaman lafiya ba."
"Dole ne a haɗa dukkan masu ruwa da tsaki a cikin wannan yunƙurin samar da sulhu. Ba wanda za a bari a baya. Idan aka bar wani, to ba cikakken zaman lafiya bane."
“Dole ne ƴan majalisar dokoki ta jiha da ta tarayya su kasance cikin tsarin. Dole ne jam’iyyun siyasa biyu su kasance cikin lamarin."

"Sauran shugabanni ma dole a shigar da su. Idan hakan ta faru, za mu san cewa an shirya gaskiya wajen maganar zaman lafiya."

Wike ya caccaki jam'iyyar PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki jam'iyyarsa ta PDP mai hamayya.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana cewa ko kaɗan jam'iyyar PDP ba ta shirya tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 ba.

Wike ya nuna cewa PDP ba ta da wani ingantaccen tsari wanda zai sanya ta iya ƙalubalantar jam'iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng